Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Kwalejin Kimiyyar Jinya da Ungozoma ta Jihar Kano (Kano State College of Nursing Sciences), ƙarƙashin jagorancin Dakta Bara’atu Gwadabe, ta gudanar da bikin yaye ɗalibai sama da 300 da suka kammala karatunsu a fannonin jinya da ungozoma.
Shugabar kwalejin ce ta bayyana hakan yayin jawabinta a bikin yaye ɗaliban da aka gudanar ranar Laraba a babban harabar makarantar da ke kusa da Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH), a birnin Kano.
ɗaliban da aka yaye sun fito ne daga babban harabar kwalejin da ke Kano da kuma sauran rassanta da ke Danbatta, Gwarzo da Madobi. Gwamnatin Jihar Kano ta kafa rassan domin samar da isassun ma’aikatan jinya da ungozoma a jihar.
A jawabinta, Dakta Bara’atu ta bayyana cewa an bai wa ɗaliban horo mai kyau tare da tarbiyyar da ta dace da aikin jinya da ungozoma.
Ta kuma ja hankalin iyaye da ɗaliban da aka yaye cewa aikin jinya sana’a ce da ke buƙatar sadaukarwa da taimakon al’umma, musamman a yankunan karkara, inda ake fama da ƙarancin ma’aikatan lafiya idan aka kwatanta da birane.
Shugabar kwalejin ta yaba wa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, kan ci gaban da aka samu a kwalejin da sauran cibiyoyin kiwon lafiya da ilimi, tare da sauran fannoni na rayuwar al’ummar jihar.
Ta kuma yaba wa Dakta Zawaciki bisa ƙoƙarinsa na ganin an samu ɗimbin ɗaliban da suka kammala horo a fannin kimiyyar jinya da ungozoma a wannan karon, musamman daga Kumbotso, da sauran rassan kwalejin.
Ta miƙa godiya ga ma’aikatan kwalejin da sauran masu ruwa da tsaki bisa gudummawarsu wajen bunƙasa makarantar.
