Kwamitin amintattun MOPPAN sun miƙa ta’aziyyar shugaban ƙungiyar na ƙasa, Maikuɗi Cashman

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Ƙungiyar masana’antar shirya fina-finai ta Najeriya (MOPPAN) ta bayyana alhini rasuwar Shugabanta, Alhaji Umar Maikuɗi Cashman, wanda ya rasu bayan doguwar jinya a birnin Zariya. Marigayin ya samu shugabancin Ƙungiyar ne bayan nasarar da ya samu a babban taron zaɓe da aka gudanar a Lafiya, inda ya fito da sabon hangen nesa na bunƙasa Ƙungiyar da ci gaban masana’antar fim a Najeriya.

A wata sanarwa daga kwamitin amintattu na MOPPAN, an bayyana Alhaji Maikuɗi a matsayin jajirtaccen shugaba wanda ya bayar da gagarumar gudunmawa tun daga lokacin da yake a matsayin mamba na kwamitin zartarwa. Ya wakilci Ƙungiyar a taruka da dama tare da shugabanni masu tasiri a masana’antar, yana nuna ƙwarewa, sadaukarwa da kishin ci gaban al’umma. Rashinsa babban giɓi ne da ba zai cika da sauki ba.

Ƙungiyar ta miƙa saƙon ta’aziyya ga dukkan mambobin MOPPAN, masana’antar fina-finai ta Najeriya baki ɗaya, da kuma iyalan marigayin. MOPPAN na rokon Allah Maɗaukakin Sarki ya gafarta masa, ya sa kabarinsa ya kasance lambun Aljanna, Ya kuma ba dangi da abokan arziki haƙurin jure wannan rashi. Kungiyar ta ce za a ci gaba da tunawa da irin gudunmawar da Alhaji Maikuɗi ya bayar a tarihin MOPPAN da masana’antar fim gaba ɗaya.

By ukarofi