Lauyoyi sun musanta zargin raba Dala 2,000 ga manyan lauyoyi a taronsu na Maiduguri

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kungiyar Lauyoyin Nijeriya (NBA) ta yi watsi da zargin cewa, an raba dala 2,000 ga wasu manyan lauyoyi masu muƙamin SAN a matsayin “kuɗin halarta” yayin taronta na baya-bayan nan a Maiduguri, tana mai bayyana iƙirarin a matsayin mara tushe kuma ba tare da wata hujja ba.

Taƙaddamar ta biyo bayan taron Kwamitin Zartarwa na ƙasa (NEC) na ƙungiyar da aka gudanar a jihar Borno, inda aka fara yaɗa jita-jitar cewa an biya wasu manyan lauyoyi kuɗi da dala a ɓoye.

Wannan batu ya janyo muhawara mai zafi a tsakanin lauyoyi da jama’a, tare da zubar da inuwa kan sahihancin taron.

Sai dai a wata sanarwa da sakatariyar ƙungiyar ta fitar, NBA ta bayyana ƙarara cewa ba ta karɓi kowane irin kuɗi ba, balle ta ba da izinin rarraba irin wannan adadi ga kowa.

“ƙungiyar ba ta karɓawa, kuma ba ta amince da rabon wani irin kuɗi ba,” inji sanarwar.

ƙungiyar ta ƙara da cewa, babu wata takardar biyan kuɗi, jadawalin rabon kuɗi daga gwamnatin jihar, jerin sunayen waɗanda aka bai wa kuɗin, ko wani ɓangare a kasafin kuɗi da zai nuna an aiwatar da irin wannan biyan.

Shugaban NBA, Afam Osigwe (SAN), shi ma ya mayar da martani kan zargin, yana mai cewa babu wani kuɗi na ƙungiyar da aka karkatar, aka yi amfani da shi ba bisa ƙa’ida ba, ko aka raba wa kowa yayin taron Maiduguri.

A cewarsa, duba bayanan kuɗin shiga da fita na ƙungiyar bai nuna wata mu’amala da ta shafi dala dala 2,000 ba.

Har ila yau, ya yi ƙarin haske kan jita-jitar da ta shafi halartar Gwamnan Jihar Borno a wajen liyafar da aka shirya a lokacin taron, yana mai cewa gwamnan bai gabatar da jawabi ko wata kyauta ta kuɗi ba a wajen.

NBA ta jaddada cewa halartar jami’an gwamnati a irin waɗannan taruka ba ya nufin an yi wata badaƙala ko cin hanci, tana mai gargaɗin cewa yaɗa labarai ba tare da hujja ba na iya ɓata sunan shugabanni da manyan lauyoyi.

ƙungiyar ta ƙara da cewa, duk wani zargi da ya shafi amfani da kuɗaɗen jama’a ana iya bincikarsa ta hanyoyin da doka ta tanada, ciki har da yin amfani da Dokar ‘Yancin Samun Bayanai (FOI). Sai dai har yanzu, babu wata hujja da aka gabatar da za ta tabbatar da zargin raba dala dala 2,000.

Duk da hayaniyar da batun ya haifar, NBA ta tabbatar da cewa kundin kuɗinta a buɗr yake kuma shugabanninta sun yi aiki da cikakken bin ƙa’ida da ɗa’a.

By ukarofi