
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Isyaka Rabe, ɗan marigayi Manjo-Janar Rabe Abubakar (mai ritaya) da ya rasu a hannun ‘yan bindiga a kwanan nan, ya yi watsi da iƙirarin cewa mutuwar mahaifinsa ta faru ne sakamakon tashin “ciwonsa na cutar suga ko hawan jini”.
A wata hira da manema labarai a ranar Lahadi, Isyaka ya bayyana rahotannin da ke alaƙanta rasuwar mahaifinsa da cutar suga a matsayin abin da ba haka yake ba, yana mai cewa iyalansa ba su yarda cewa irin wannan rashin lafiyar ne sababin mutuwar tsohon sojan ba.
Kalaman nasa na zuwa ne kwanaki kaɗan da Gwamnatin Jihar Katsina ta sanar da cewa marigayin ya rasu ne a hannun ‘yan bindiga inda ta danganta hakan da cutar suga da hawan jini.
Saidai Isyaka ya yi watsi da waɗannan dalilai, inda ya ce mahaifinsa ba shi da cutar suga ko hawan jini kafin a yi garkuwa da shi.
“Mahaifinmu bai kasance mai cutar suga ko hawan jini ba. Mutane suna da mabanbanta ra’ayoyi akan abin da ya faru,” inji shi.
A cewarsa, duk da cewa har yanzu ba a gano ainihin abin da ya sabbaba mutuwar marigayin ba, iyalan na tunanin ta yiwu ya rasu ne saboda cizon maciji.
Ya ƙara da cewa, wasu na tunanin ƙila ya taka wani abin cutarwa ne a hannun ‘yan bindigar, yana mai cewa an fitar da wani faifan bidiyo daga ‘yan bindigar bayan zargin cizon maciji, amma babu tabbas akan haka.
Kazalika, ya bayyana marigayin a matsayin jajirtacce, mai kawaici kuma mai son zaman lafiya da ya rayu cikin mutunci, sannan ya rasu a matsayin gwarzo.
Har ila yau, iyalan tsohon sojan sun ce ba su san yadda aka karɓo gawarsa ba daga hannun ‘yan bindigar ba.
Isyaka ya kuma ƙaryata batun da ke yawo a kafafen sada zumunta na cewa, mahaifiyarsa da ke hannun ‘yan garkuwar ta shaƙi iskar ‘yanci.
