Daga RABIU SANUSI a Kano
Uban ƙasa, Mai martaba HRH Engr. Saleh Muhammad Umar, OON (Mai Kaltungo), ya halarci bikin cikar Mai Martaba Sarkin Keffi, HRH Dr. Shehu Chindo Yamusa III, shekaru goma a kan karagar mulki.
Engr. Saleh Muhammad Umar, wanda shi ne North East Coordinator na NTRC da kuma Mataimakin Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Gombe ya wakilci masarautar Kaltungo tare da tawagarsa a wannan gagarumin biki.
Bikin ya gudana ne a harabar Kwalejin Gwamnati da ke birnin Keffi, inda ya samu halartar manyan sarakuna daga Jihar Nasarawa da ma sauran sassan kasar nan, tare da ‘ya’yan masarautar Keffi, ‘yan siyasa, ‘yan kasuwa da al’umma.
An gudanar da taron cikin tsari mai ƙayatarwa. A yayin bikin, Mai Kaltungo ya taya Sarkin Keffi murnar cika shekaru goma yana jagorantar al’ummarsa cikin zaman lafiya, adalci da tausayi.
Engr Saleh Muhammad ya kuma yi masa fatan alheri da addu’ar Allah Ya kara masa tsawon rai, lafiya da hikima, tare da fatan Allah Ya sake kai shi ga wasu karin shekaru masu yawa yana hidimtawa al’umma.
An kammala bikin da addu’o’in fatan alheri, tare da rokon Allah Ya dawo da Uban Kasa Mai Kaltungo da tawagarsa gida lafiya cikin aminci.
