Mai yiwuwa ne matakan Sin na iya maida komaɗar tattalin arzikin duniya

Daga AHMAD FAGAM

A yayin da tattalin arzikin duniya ke cikin halin rashin tabbas a sakamakon tarin matsalolin da suka yi masa dabaibayi, haƙiƙa, tattalin arzikin duniya yana fama da wahalhalu a wannan lokaci.

Koda yake, mai yiwuwa ne tattalin arzikin duniyar zai iya samun sassauci gami da farfaɗowa a sakamakon wasu jerin matakan da ƙasa ta biyu mafi ƙarfin tattalin arziki a duniya ke ɗauka, waɗanda suka shafi matakan daidaita yanayin tattalin arzikin ƙasar na cikin gida kuma ka iya yin tasiri ga bunƙasar tattalin arzikin duniya baki ɗaya.

A ƙarshe wannan mako ne, babban bankin duniya ya fitar da sabon rahoto kan tattalin arzikin ƙasar Sin, inda mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Zhao Lijian ya yi tsokaci kan wannan batu, inda ya bayyana cewa, yayin da ake fuskantar ƙalubale daban-daban a cikin gida da kuma waje, tattalin arzikin ƙasar Sin zai iya tabbatar da daidaito da samun ci gaba na dogon lokaci da ma ba da ƙwarin gwiwar daidaitawa da farfaɗo da tattalin arzikin duniya.

Sabon rahoton tattalin arzikin Sin din da babban bankin duniya ya fitar ya nuna cewa, a cikin rubu’in farko na wannan shekara, tattalin arzikin ƙasar Sin ya samu bunƙasa sosai.

Biyo bayan wasu tsare-tsare da matakai na daidaita tattalin arziki, ana sa ran saurin bunƙasuwar tattalin arzikin ƙasar Sin ya sake dawowa a cikin rubu’i na biyu na wannan shekara.

Ita ma babbar hukumar kwastom ta ƙasar Sin GAC, ta sanar da cewa, a watanni biyar din farko na shekarar 2022, hada-hadar cinikayyar ƙasashen waje na ƙasar Sin ya samu ƙarin kashi 8.3 bisa 100, idan an kwatanta da makamancin lokacin bara inda adadin ya karu zuwa RMB yuan triliyan 16.04. Ta fannin dalar Amurka kuwa, jimillar cinikayyar ƙasashen wajen ya kai dala triliyan 2.51 a cikin watannin biyar, inda ya ƙaru da kashi 10.3 a bisa na makamancin lokacin bara.

A cikin wannan wa’adi kuma, cinikayyar ƙasar Sin da manyan abokan hulɗar kasuwanci uku, wato ƙungiyar ƙasashen kudu maso gabashin Asiya, da ƙungiyar tarayyar Turai, da kuma Amurka, ya ƙaru da kashi 8.1 bisa 100, da kashi 7 bisa 100, da kuma kashi 10.1 bisa 100, idan an kwatanta da shekarar da ta gabata.

Daga watan Janairu zuwa Mayu, hulɗar kasuwancin Sin da ƙasashen dake bin shawarar “ziri ɗaya da hanya ɗaya”, ya karu zuwa kashi 16.8 bisa 100 a bisa na makamancin lokacin bara, inda ya karu zuwa RMB yuan triliyan 5.11.

Abin da ya bayyana a fili shi ne, an samu farfaɗowar ne bayan da gwamnatin ƙasar Sin ta dauki matakan tallafawa kamfanonin ƙasashen ketare, wajen rage musu wahalhalu a sakamakon ɓarkewar annobar COVID-19 a cikin gida, da kuma rashin tabbas a yanayin tattalin arzikin ƙasashen ƙetare.

A cewar Li Kuiwen, jami’in babbar hukumar GAC, ƙasar Sin ta ɓullo da wasu jerin matakan daidaita yanayin tattalin arziki, da kuma inganta yanayin kasuwancin waje a cikin wannan shekarar, matakan waɗanda dama an yi tsammanin za su taimaka wajen saurin farfaɗowar tattalin arzikin da zarar suka fara aiki. Ko shakka babu, waɗannan wasu alamu ne a bayyane dake ƙara nuna tasirin matakan da ƙasar Sin ke ɗauka wajen daidaita yanayin tattalin arzikinta waɗanda ba kawai suna amfanawa ƙasar kadai ba ne, har ma suna ƙara samar da tabbaci ga ci gaban tattalin arzikin duniya.

Fassarawa: Ahmad Fagam