Samun ci gaba na buƙatar hangen nesa

Daga BELLO WANG

Shugaba Muhammad Buhari na Najeriya ya yi jawabi na musamman a jiya ranar Dimokuraɗiyya, inda ya jaddada alƙawarin tabbatar da tsaro a ƙasarsa. Kana a nasu ɓangare, jama’ar ƙasar sun ci gaba da nuna damuwa kan matsalolin rashin ayyukan yi, da tsadar rayuwa, a shafukan sada zumunta, inda suka bayyana koma bayan tattalin arziki a matsayin babban dalilin da ya haddasa rashin kwanciyar hankali a wasu wuraren ƙasar.

Abin lura shi ne, ba Najeriya ce kadai ke fuskantar matsalar tattalin arziki ba. A halin yanzu, annobar COVID-19 da yakin da ake yi tsakanin Rasha da Ukraine, sun jefa tattalin arzikin duniya cikin wani yanayi na rashin tabbas. Idan muka dubi alƙaluman da aka samu a kwanakin nan, za mu ga jimillar GDP ta ƙasar Amurka ta ragu da kaso 1.4, sa’an nan yadda bankin tsakiya na ƙasar ya ɗauki matakai don daidaita matsalar hauhawar farashin kayayyaki, ya sa kasuwar hannayen jari ta ƙasar ta gamu da babbar matsala, inda farashin kusan dukkan hannayen jari ya ragu sosai.

Yayin da a ƙasar Birtaniya, hauhawar farashin kayayyaki ta sa bankin Ingila ya daga jimillar ruwan da ake bayar kan kuɗin ajiya zuwa wani matsayin da ba a taba ganin irinsa ba cikin wasu shekaru 13 da suka wuce, tare da sanar da taɓarɓarewar tattalin arzikin kasar. A cikin wannan yanayi mai wuya da ya shafi dukkan ƙasashe, ya kamata a yi ƙoƙarin yin hangen nesa, da ɗaukar nagartattun matakai, da haɗin gwiwa da sauran ƙasashe yadda ake bukata.

Dole ne a magance matakai na son kai, da ma rashin hangen nesa. Misali, a Najeriya, wasu matasa sun ɗauki makamai sun zama ‘yan fashi sakamakon kwaɗayi. Amma idan ana da hangen nesa, za a iya ganin cewa ayyukan da suke yi sun haifar da ɓarna ga jama’a, kana nan gaba tabbas za a yanke musu hukunci bisa muggun ayyukan da suka aikata.

Ban da wannan kuma, misali a ƙasar Amurka, gwamnati ta bari cutar COVID-19 ta haddasa asarar rayukan mutane fiye da miliyan 1, da raunana tattalin arziki, tana neman raya tattalin arzikin ƙasar ta hanyar zuba maƙudan kuɗi cikin kasawanni kawai amma ba tare da ɗaukar matakai na hana bazuwar annoba ba, abun da ya sa ake fama da matsalar hauhawar farashin kayayyaki mai tsanani a ƙasar.

Sa’an nan, wasu ƙasashen yammacin duniya, yayin da suke fuskantar koma bayan tattalin arziki, suna neman ta da rikici tsakanin sauran ƙasashe, da raunana tattalin arzikinsu, don neman sanya karin jari komawa cikin kasuwannin gida. Amma a haƙiƙa, bayan an samu ɓarkewar yaƙi a wani yanki, lamarin ya kan kawo cikas ga aikin samar da kayayyaki na duniya, da haifar da illa ga tattalin arzikin ƙasashe daban daban.

Dalilin da ya sa ƙasar Sin ke iya samun ci gaban tattalin arzikinta cikin matuƙar sauri, cikin shekaru fiye da 40 da suka wuce, shi ne domin hangen nesa da ta yi, abin da ya sa take iya ɗaukar nagartattun matakai masu ɗorewa, da daidaita moriyarta da ta sauran ƙasashe. Yayin da take hulɗa da ƙasashen Afirka, ƙasar Sin ta tsayawa kan manufar “tabbatar da daidaito, da moriyar dukkan ɓangarori”.

Tana fatan ganin ƙasashen Afirka sun samu ci gaban tattalin arizki, kana tana goyon bayan haɗin gwiwar da kasashen Afirka suke yi da sauran ƙasashe. Idan mun dauki bashin da ƙasar Sin ta ba ƙasashen Afirka a matsayin misali, za mu ga cewa, ko da yake kafofin watsa labaru na ƙasashen yamma su kan bayyana shi a matsayin “mulkin mallaka” da “tarkon bashi”, a haƙiƙa ƙasar Sin na ba da bashi ne bisa ainihin buƙatun da kasashen Afirka suke da shi, da taimakawa ƙasashen Afirka inganta kayayyakin more rayuwa:

Tun daga shekarar 2000, kamfanonin ƙasar Sin sun taimaki ƙasashen Afirka wajen gina ko kuma inganta layin dogo na fiye da kilomita dubu 10, da hanyoyin mota kimanin kilomita dubu 100, da gadaje kimanin dubu 1, da tashoshin jiragen ruwa 100, dai dai sauransu. Sa’an nan idan wata kasa ta gamu da matsalar biyan bashi, ƙasar Sin za ta tattauna da ita don samar da wata dabara mai dacewa don daidaita batun, har ma ta kan yafe wa ƙasashen maras karfi bashin da take binta.

Hangen nesa ne ya sa ƙasar Sin take son zuba jari don tabbatar da ci gaban tattalin arzikin ƙasashen Afirka, gami da ba da damar samun ci gaban harkoki ga kamfanonin ƙasar.

Fassarawa: Bello Wang