AFCON 2023: Nijeriya ta lallasa Sao Tome da ci 10-0

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A cigaba da buga wasannin neman cancantar buga kofin nahiyar Afirka (AFCON), tawagar Nijeriya ta Super Eagles ta lallasa takwararta ta Sao Tome da Principe da ci 10 ba ko ɗaya.

A wasan dai wanda aka fafata ranar Litinin, ɗan wasan Nijeriya Victor Osimhen ne ya ci wa Super Eagles ƙwallo huɗu shi kaɗai.

Osimhen ya fara zura wa Nijeriya ƙwallo ta farko ne a minti na tara da fara wasan, kafin ya taimaka wa Moses Simon da Terem Moffi su ma su zura nasu ƙwallayen a mintuna na 28 da na 43.

Ya kuma ƙara ƙwallonsa ta biyu a ragar abokan hamayyar nasu a minti na 48, sannan ya ƙara ta uku a minti na 65.

Osimhen, wanda ɗan wasan gaba ne a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Napoli da ke ƙasar Italiya ya ci ƙwallonsa ta huɗu ne a minti na 84, lamarin da ya kawo adadin ƙwallayen da Nijeriya ta ci zuwa biyar.

Shi kuwa Terem Moffi ya ci ƙwallonsa ta biyu ne a minti na 60, sai Oghenekaro Etebo da Dennis Emmanuel da kuma Lokman Ademola su ma suka zuzzura ƙwallo ɗai-ɗaya.