Wani mutumi ya maka jaruma Gabon kotu kan ƙin amincewa da aurensa

Wani mutumi ya maka jaruma Gabon kotu kan ƙin amincewa ya yi wuf da ita

Daga AISHA ASAS

Wani ma’aikacin gwamnati, mai kimanin shekaru 48 a duniya, mai suna Bala Musa, ya maka fitacciyar jaruma a masana’antar Kannywood Hadiza Gabon kotun shari’ar Musulunci a Kaduna, don qin amincewa da ƙoƙon baransa na zama maigidanta.

Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa, lamarin ya faru ne a ranar Litinin ɗin da ta gaba ne, inda Bala Musa ya gurfanar da jaruma Gabon gaban alƙali, kan ƙin amincewa su yi wuf da juna.

Mai ƙarar ya sanar da kotu cewa, sun jima suna suburbuɗa soyayya da jarumar, har ta kai ta masa alƙawarin za ta aure shi.

”Na jima ina ɗawainiya da ita, zuwa yanzu na kashe mata zunzurutun kuɗi, wuri na gugan wuri har N396,000. A duk lokacin da ta neme ni kuɗi, bana ƙiya mata, saboda ina fatan ta cika min alƙawarin da ta ɗaukar min na aure,” a cewar Bala.

Ya kuma ƙara da ƙorafin rashin kawo masa ziyara a garin Gusau na Jihar Zamfara kamar yadda ita ta kwaɗaita masa. “kuma ta kasa cika min alƙawarin ziyara da ta yimin a garin da na ke, wato Gusau, duk da cewa na yi shiri na musamman domin tarbon ta,” inji shi.

Kamfanin dillancin labarai (NAN) ya ruwaito cewa, ba a wannan rana ta Litinin ce aka fara wannan fafatawa tsakanin jaruma Gabon da masoyin na ta ba, domin an fara sauraron ƙarar ne tun a 23 ga watan Mayu, duk da cewa wadda ake ƙarar bata samu halarta ba, yayin da lauyanta Mubarak Kabur ya wakilce ta.

Da yake mayar da martani, lauyan jarumar ya buƙaci kotu ta duba matsayin wadda yake karewa da kuma irin shuhura da take da ita, wanda hakan kawai zai iya zama sanadiyyar faruwan wannan ƙarar ko da kuwa babu gaskiya a cikinta.

Ya kuma ƙara da nema mata gafarar kotu kan rashin halartar zaman, a cewarsa tana taka-tsantsan ne kan lafiyarta kan sha’ani na matsalar tsaro. Ya kuma nemi alfarmar kotu ta ba shi wata dama don tabbatar da ya kawo wadda yake kare wa a zama na gaba.

Daga ƙarshe, alƙalin da ke jan ragamar wannan ƙara, Malam Rilwanu Kyaudai ya ɗage sauraren ƙarar har zuwa 13 ga watan Yuni, inda ake fatan wadda ake ƙara ta bayyana a gaban kotu.