Na amince ina da matsalar ƙwaƙwalwa, don haka zan nemi taimako, cewar jarumi Terry Crews

Daga AISHA ASAS

Ɗaya daga cikin baƙaƙen da suka yi babban tsalle a masana’antar finanfinai ta Hollywood kuma masana’antar ta ke ji da alfahari da su, Terry Crews, ya yaye labule kan lamarin da ya shafi lafiyarsa, inda ya bayyana wa duniya cewa, a yanzu ya amince ƙwaƙwalwarsa ba a saite take ba, don haka yana buƙatar taimako.

Jarumin da yafi ƙarfi a ɓangaren barkwanci ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da Amy Morin, ya bayyana cewa, a yanzu ya gaji da yawo da nauyin da yake kan kafaɗarsa na matsalolinsa, don haka zai fara zuwa ganin likita don tattauna matsalolinsa da kuma ba shi mafita kan su wato therapy a turance.

Crews wanda ya kasance tsohon ɗan wansa a NFL ya ce, ya yi fama da matsin lamba a rayuwarsa, kan sha’anin da ya jivinci nauyi da ya rataya kan sa, wannan kuwa ya zama sila na lahanta lafiyar ƙwaƙwalwarsa da kuma rayuwar aurensa.

”Tsayin shekaru 40 na yi su ne bisa yaƙi da rayuwa, don ganin na riga kowa miƙewa, na yi aiki fiye da saura kuma in tabbatar na fi kowa yawan aikin. Wannan ya bada gudunmuwa wurin sanyaya ƙarfin batirin ƙwaƙwalwata, idan muka yi duba da matsin lambar da ke cikin duniyar wasanni da kuma harkar nishaɗantarwa. Wannan kawai zai iya cinye lafiyar ƙwaƙwalwa tun da wuri.”

Terry ya bayyana dalilinsa na saranda ya amince da yana buƙatar taimakon ta ɓangaren lafiyarsa, inda ya faɗa cewa, sai da ya canza wa kalmar jarumta ma’ana daga irin ma’anar da ya bata ta farko kafin ya amince yana buƙatar taimakon wani.

“Sai da na sauya wa kalmar jarumta suna kafin in amince da ina da abin da abaya na ɗauka a matsayin rauni. A baya ma’anar jarumta a wurina shine, ƙarfin iya naushi a cikin kowanne al’amari, amma a sabon fahimtar ma’anar kalmar da na yi shine, samun damar iya ɗaukar rayuwa da sauƙi, juriya kan matsalolin da kake fuskanta tare kuma da amincewa kana da rauni, kuma nuna rauninka bai zama illa ba.”

Jarumin ya jinjina nauyi da amfanin ganin likita a lokaci na damuwa, ya kuma bayyanashi a matsayin hanya ta ceto rayuwa, ya kuma amince a baya yana layin waɗanda ke kallonsa da muni.

“Tarafi(therapy) cikas ne ga rayuwa a irin al’ƙaryar da na ta so a ciki. Ana yi masa kallon aibu tare da aibata duk mai zuwa yinsa, saboda ana danganta shi da hauka. A lokacin da ka sanar da wani damuwarka da irin tunanin da kake yi, zai zama tamkar kana magana da kanka, wanda zai zama wani nau’i na hauka, a irin fahimtar da muke da ita kan sa.”

Wannan ma’anar da mutanen jarumin ke da kan sha’ani na zuwa neman taimako kan matsala ta damuwa ne ya hana jarumi Terry neman taimako da wuri, har matsalarsa ta yi nisan da ta sa shi asarar muhimman mutane a rayuwarsa.

Jarumin ya bayyana cewa, sai da ya rasa matarsa ne ya gano nisan kiwo da ya yi da kuma illar da matsalarsa ta yi masa, a lokacin ne ya amince da yana da matsala tare kuma da gane buƙatar da yake da na neman taimakon matsalarsa. Ya kuma bayyana jin daɗinsa kan buɗe masa ido da wani abokinsa ya yi yayin da ya fallasa masa sirrin zuciyarsa.

“Ya ce, Terry ba zan maka alƙawarin nema ma ka mafita kan matarka ta dawo gare ka ba, sai dai mafita kan yadda za ka samu sauƙin kan ka. Wannan furucin na sa ya yi tasiri sosai a rayuwata ta yanzu, duba da cewa a baya rayuwata ta tattara ne kan me zan samu bayan kowanne abu da na ke yi, zan samu kaza idan na aikata kaza. A yanzu na fahimci wannan ba ya da tasiri a rayuwar ɗan Adam, ban kuwa gane hakan ba sai da na mallaki kusan komai da na ke son samu, duk da na mallake su, ina jin kai na ban cika ba. Matata ta bar ni, na rasa iyalina duk da cewa na samu shahara, ina jin kaina ba komai ba.”