Masu ba da taimako na Ƙasar Sin sun bayar da ƙwarin gwiwa ga ɗalibai matasa na makarantun Kenya

Daga CMG HAUSA

Masu bayar da taimako na ƙasar Sin suna bayar da ƙwarin gwiwa ga matasan dake karatu a makarantar Mcedo Beijing dake yankin Mathare a Nairobi, babban birnin ƙasar Kenya.

Yaran waɗanda marasa galihu ne, sun samu damar shiga makarantar wacce ke yankin gabashin birnin Nairobi, sun yabawa taimakon da suka samu daga masu bada taimako na ƙasar Sin, inda aka kashe musu kishirwar da suka shafe shekaru da dama tana damunsu na burin samun ingantaccen ilmi.

Naftali Kizito, wani dalibin aji na 8 na makarantar Mcedo Beijing, ya faɗawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a lokacin tattaunawar da aka yi da shi a baya bayan nan cewa, taimakon da ƙasar Sin ta bayar ya sauya yanayin makarantarsu, inda ta koma wata cibiyar koyarwa irin ta zamani.

Kizito ya ce, gabanin bayar da gudunmawar, dakunan karatun da suke amfani da su na wucin gadi ne. A yanzu an yi musu gine-gine waɗanda suke jin dadin koyon karatu a cikinsu.

A shekarar 2007, ofishin jakadancin ƙasar Sin a Kenya ya samar da kuɗaɗen gudanar da aikin gina makarantu na zamani a makarantar Mcedo Beijing.

Daga bisani a shekarar 2012, sakamakon shirin da ofishin jakadancin Sin ya ɓullo da shi a Kenya, kungiyar haɗin gwiwar bunƙasa tattalin arziki da kasuwanci ta Sin da Kenya wato (KCETA), ta tsara wasu kamfanonin ƙasar Sin ta dama, kana ta samar da kuɗaɗen tallafawa aikin faɗaɗa makarantar.

Mai fassara: Ahmad