Yajin Aiki: Gwamnati, ASUU da daginta sun koma teburin sulhu

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Tarayya ta koma teburin sulhu don ci gaba da tattaunawa tsakaninta da ma’aikatan jami’o’in Nijeriya.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, kamata ya yi kwamitin sulhun da gwamnatin ta kafa a ce ya kammala aikin sulhunta tsakanin ɓangarorin da lamarin ya shafa tun a ranar 7 ga Yuni, 2022 amma hakan bai yiwu ba.

Sai dai, sahihan bayanai sun tabbatar cewa ɓangaaren ƙungiyoyin da lamarin ya shafa zai gana da gwamnati a wannan Litinin ɗin, yayin da wani sashen zai gana da Gwamnatin a Juma’a mai zuwa.

Wata majiya ta kusa da ASUU ta ce, “Za mu gana da Gwamnatin Tarayya ranar Litinin.”

Haka ma an ruwaito Shugaban ASUU na Ƙasa, Farfesa Emmanuel Osodeke na cewa, za su ci gaba da tattaunawa a cikin wannan makon.

“Za mu ci gaba da tattaunawa wannan makon kuma mun samu gayyatan hakan wannan makon. Za a iya cimma ƙarshen sulhun ne idan muka janye yajin aiki.

“Da yake muna ci gaba da yajin aikin namu, ba za a daina tattaunawar ba. Ba mu da wata matsala da kwamitin. Idan kuwa muna da ita, za mu tuntuɓi kwamitin,” inji Osodeke.

A hannu guda, Shugaban SSANU na ƙasa ya ce, Juma’a mai zuwa ɓangarensu zai gana da Gwamnatin Tarayya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *