Shin mijinki ya cancanci girmamawa? (2)

Daga AISHA ASAS

Mai karatu barkanmu da sake saduwa a shafin iyali na jaridar al’umma, Manhaja. Godiya ta musamman gare ku masu bibiyar mu. Allah ya ƙara mana zaman lafiya a gidajen aurenmu.

A satin da ya gabata, idan ba ku manta ba, mun kawo wasu daga cikin dalilan da ke zubar da ƙimar mazaje a idon matansu. Har muka gangara kan bayyanai kan kallon da ake wa mace a Ƙasar Hausa. Alƙalamin na mu ya tsaya ne kan tambaya, bayan tattaro bayyanai da hujjojin da ka iya kai mace ga qin girmama mijinta, sai dai waɗannan dalilai za su iya zama hujjar da mijinki zai cancanci wulaƙantawa?

A farko mun kawo hadisi ingantacce da ya nuna daraja da ƙima da miji yake da wurin matarsa, sai dai har na kai ƙarshen hadisin ba inda Annabin rahma ya kawo sharaɗin da sai miji ya cika shi ne zai samu girmamawa daga wurin matarsa.

Alqur’ani mai tsarki ya faɗa, “ku yi mu’amala da su bisa kyautatawa” (mata). Idan mijinki bai aikata hakan ba, wa ya sava wa? Ina ce umurnin ubangijinshi. To ke kuwa idan sanadiyyar muzgunawar da yake maki kuma kika fara yi masa rashin mutunci, me kika aikata? Ina ce kun zama ɗaya kenan. Bai ji maganar Ubangiji ba, kema ba ki ji ba.

Duk da cewa, Musulunci bai ce dole sai kin ɗauki kowanne irin cin kashi daga mijinki ba, sai dai ba inda aka ba ki damar yi masa rashin mutunci ko wulaƙanta shi ba.

A wannan lokaci da muke ciki ba maza ne kawai ba su san darajar mata ba a Ƙasar Hausa ba, har da matan. Maganar gaskiya lokuta da dama idan ɓera na da sata, dadawa ma da warinta. Mata da dama ba sa ba wa mazajensu girma da darajar da Allah ya ba su. Zuciyarmu ta gurvata da furucin da muke wa laƙabi da wayewa wato “abin da namiji zai yi, mace za ta iya yin fiye” wannan kalamin ne ya yi tasiri a zukatan mata da yawa, har suke ganin ba sa buƙatar ba wa miji wani girma na musamman, domin matsayi ɗaya suke da shi.

Ta wannan furuci ne suka aminta duk abin da suke son su yi, mazajensu ba su isa su hana su ba, idan sun yi yunƙurin yin haka kuwa, to fa sun fara cin zarafin mace ne, sai ki shiga raratawa tare da shelanta wa duniya don ta kawo ma ki ɗauki.

Har wa yau, albarkacin wannan zuga ta sheɗan ne, matar aure ke jin girman kai kan ba wa mijinta haƙuri idan ta yi masa laifi. Don tana ganin ba abin da ya fita, a wasu ɓangarorin ita ce ya kamata ta fi shi.

Ya ke ‘yar’uwa, shin kin manta da hadisin Manzo tsira da yake cewa, ” mace ‘yar aljanna ita ce, wadda ke ba wa mijinta haƙuri a lokacin da ta yi masa laifi da kuma lokacin da ya yi mata laifi.” Shin kina da wani buri a matsayin ki ta mace Musulma da ya wuce shiga aljanna?

Duk yadda kike ganin zamani ya ɗaure ma ki gindi wurin wulaƙanta ƙima da darajar aure, ba zai iya kare ki daga girban abin da kika shuka tun a nan duniya.

Me muke nema ne da addinin Musulunci bai ba mu ba na ‘yanci ya ku ‘yan’uwa. Babu shakka Musulunci ya wa mata gata tare da ba su ‘yanci mai tarin yawa, sai dai idan rashin ilimi ya hane mu da ganin su. Daraja mace tare da kare haƙƙoƙin ta ba kamar addinin Musulunci, idan muka yi duba, muka karanta hukunce hukuncen da suka rataya ga iyaye kan ‘ya’yansu mata da kuma mazaje kan matayensu, za mu tabbatar duk wani tsarkakaken ‘yanci mace ta same shi a addinin Islama.

Idan kuwa haka ne, me zai sa mu bijirewa Ubangijinmu ko dan nuna godiyar mu gare shi. Babu wani girmamawa da mutuntawa da addini ya ce ki yi wa mijinki da bai ce shima ya ma ki irinsa ba, bambancin kawai, shi an sanya shi ya zama shugaba gare ki, ya zama sama da ke, don a samu daidaito a tafiyar rayuwa. Kuma hakan idan kin yi dogon nazari za ki samu cikin waɗanda hakan zai ribanta kina cikin layin farko, don haka Musulunci ba cutar da ke ya yi ba ta wannan ɓangare.

Ya ku ‘yan’uwa mata, ku ji tsoron haɗuwar ku da Mahalicci a yayin mu’amala da mazajenku. Ku dinga sara kuna duban bakin Gatari, domin lallai bijire wa miji na da sakamako tun a nan duniya kafin a je lahira.

Ku tuna irin bauta da gallazawa da mata suke ciki kafin zuwan Musulunci, kai har ma a yanzu cikin wasu ƙabilun za ka samu hakan, ku kwatanta da irin rayuwar da Musulunci ya shimfiɗa ma ku, damar da ya ba ku da kuma ‘yancinku da ya ƙwato ma ku.

Ta hanyar bin umurnin ubangijin kan mu’amalar aure ne kawai za ki samu damar ganar da mijinki idan yana ma ki ba daidai ba, domin idan kin rama taƙwarƙwara ina kika ga bakin mayar da magana ko ƙorafi, kinga kuwa za ku ta yin rayuwar ne cikin ƙunci, kuma ke za ta fi cutarwa, domin shi yana da dama kan wasu matan bayan ke.

Amfanin yi wa miji biyayya tare da ba shi girma mai yawa ne ya ke ‘yar’uwa, ba za ki gane hakan ba, sai lokacin da Allah Ya gamsu da haƙurinki, Ya ji daɗin bin umurnin Sa da kika yi, to fa a lokacin za ki zama abin sha’awa da kwaɗayin rayuwar ki. Zai saka ma ki ta inda ba ki yi zato.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *