Majalisar Dattawa ta gayyaci tsohon Shugaban NNPC, Kyari da wasu kan zargin ɓatar tiriliyan N210

Spread the love

Majalisar Dattawa ta gayyaci tsohon Shugaban Babban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa NNPCL, Mele Kyari, domin amsa tambayoyi kan zargin kashe Naira tiriliyan 210 tsakanin shekarar 2017 zuwa 2023 da aka ce babu cikakken bayani game da rahoton binciken kuɗi a kai.

Haka kuma majalisar ta nemi tsohon shugaban kula da harkokin kuɗi a NNPCL, Umar Isa da kuma tsohon shugaban gudanarwa na NAPIMS, Bala Wunti su gurfana a gaban ta.

Kwamitin majalisar ya yi barazanar fitar da takardar kamu wato (warrant of arrest) idan ba su halarci zaman da za a gayyace su ba.

Shugaban kwamitin, Sanata Aliyu Wadada ɗan majalisa mai wakiltar Nasarawa ta yamma, ya ce dole NNPCL ta yi bayani kan kudaden da suka hada da; Naira tiriliyan 103 da ake zargin kashewa ba tare da wani bayani ba da kuma Naira tiriliyan 107 da aka nuna a matsayin wasu kuɗaɗen da ake bin kamfanin

Jimillar kudin da ake bukatar a yi cikakken bayani a kansu ya kai Naira tiriliyan 210.

Kwamitin ya kuma tambayi dalilin kashe kusan Naira biliyan 5 wajen canza sunan kamfanin daga NNPC zuwa NNPCL.

By Babaji