Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta buƙaci dukkan ‘yan majalisa da ke wakiltar Arewa a majalisar tarayya da su ɗauki mataki mai ƙarfi domin a soke gaba ɗaya jerin sunayen sabbin jami’an da hukumar kwastam ta ƙasa ta fitar kwanan nan.
Wannan na cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na majalisar, Kamaluddeen Sani Shawai, ya fitar a ranar Laraba.
A ƙarƙashin jagorancin Kakakin Majalisar, Rt. Hon. Jibril Ismail Falgore, majalisar ta bayyana ɓacin ran ta kan tsarin ɗaukar ma’aikatan, inda ta siffanta shi da cewa cike ya ke da son kai, nuna bambanci da rashin adalci tsakanin jihohi.
Majalisar ta ce duk da yawan jama’ar Arewa, jerin sunayen da aka fitar ya nuna cin zarafi da wulakanta tanadin dokar daidaiton ƙasa wato (Federal Character).
Da yake gabatar da ƙudirin a zaman majalisar, Jagoran Majalisa, Hon. Lawal Hussain Dala, ya ce tsarin ɗaukar ma’aikatan bai bi ƙa’idojin gaskiya da adalci ba, yana kuma ƙara rarrabuwar kai da rashin amincewa tsakanin yankuna.
Ya bayyana cewa tsarin ya nuna fifiko ga mutanen Kudu musamman yankin Kudu maso Yamma, yayin da yankin Arewa aka barshi a baya.
A cewarsa jerin sunayen da aka fitar, daga cikin jami’ai 1,785 da aka ɗauka, sama da 1,000 sun fito daga yankin Kudu, yayin da Arewa ta samu ƙasa da 540 kawai.
Majalisar ta kuma zargi hukumar kwastam da nuna fifiko ga yanki ɗaya a muhimman matakan ɗaukar ma’aikata, wanda hakan ke ƙara ta’azzarar rashin daidaito a kasar.
Da yake jagorantar zaman, Kakakin Majalisar Rt. Hon. Jibril Falgore, ya yi kira ga dukkan ƴan Arewa da ke majalisar tarayya da su shiga tsakani domin a dakatar da tsarin saboda kiyaye ɗorewar ƙasa da haɗin kai.
Kazalika ya buƙaci a bi ƙa’idojin hukumar Federal Character yadda ya kamata, tare da kira ga Shugaban Ƙasa da ya soke ɗaukar ma’aikatan gaba ɗaya, bisa hujjar cewa tsarin ya nuna rashin adalci da rashin daidaito.
Majalisar Dokokin Kano ta amince da ƙudirin baki ɗaya, inda ta nemi a soke gaba ɗaya jerin sunayen da hukumar Kwastam ta fitar a matsayin sabbin jami’an kada-kada.
