
Daga BELLO A. BABAJI
Majalisar Wakilai ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta aiwatar da dukkanin ƙarin da aka yi na kuɗaɗen fansho ba tare da jinkiri ba.
Ta yanke hakan ne bayan gabatar da batu kan kalubalen da ƴan fansho suke fuskanta a sakamakon rashin biyan su da ƙarin gami da riƙe musu sauran haƙƙoƙinsu na tsofaffin ma’aikata.
A yayin karanta batun ne a zaman majalisar na ranar Laraba, ɗan majalisa Ibrahim Ayokunle ya bayyana yadda Shugaba Bola Tinubu ya amince da ba su albashin tallafi na N25,000 da kuma ƙarin N32,000 ga kuďin fansho da tsofaffin ma’aikata suke karɓa a Nijeriya.
Ɗan majalisar ya koka game da matsalolin da tsofaffin jami’an suke fuskanta musamman a sakamakon rashin ba su haƙƙoƙin da gwamnati ta amince da su, lamarin da ke jefa su halin gaza ɗaukar ɗawainiyarsu ta yau da kullum.
Don haka ne majalisar ta buƙaci Gwamnatin Tarayya ta hannun Ma’aikatar Kuďi, hukumomin jin-ƙai, Akanta-Janar, CBN, PTAD da sauran masu-ruwa-da-tsaki da ta gaggauta fara aiwatar da sabon tsarin domin sauķaķe wa ƴan fanshon halin matsin da suke ciki.
