Marayu ‘yan makarantar firamare fiye da 500 suka amfana da riguna da littattafai a Funtua

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Marayu ƴan makarantar firamare sama da 500 ne suka amfana da tallafi littafai, riguna da jaka na makaranta wanda kwamishinan harkokin lafiya Hon Musa Adamu Funtua ta samar.

Kwamred Mannir Suleiman shugaban ƙungiyar haɗin kan Funtua wanda ya wakilci kwamishinan,ya bayyana cewa wannan tallafi kyauta ne Hon Musa Adamu ya bada domin ƙarfafa wa yara harkar ilimi da gaske.

Kwamishinan ya buƙaci masu hannu da shuni su zo su bada tasu gudunmawa domin inganta rayuwar marayu a yanki.

Ya bayyana cewa ya kirkiro da wannan tallafin marayun da daɗewa a inda ana sa ran marayu 2000 na makarantun firamare a ƙaramar hukumar Funtua za su amfana.

“Ana sa ran bama marayu ba har masu ƙaramin ƙarfi da musu buƙata na musamman za su amfana da tallafin,”inji Funtua

Hon Musa Adamu Funtua ya ƙara bayyana cewa nan bada jimawa ba zai bada wani tallafi ga ƙungiyoyin matan aure da zawarawa domin rage raɗadi.

Sai yayi kira ga ma su riƙe da muƙaman siyasa a yankin su ma su fita su bada tasu gudunmawa wajen inganta rayuwar al’ummar yankin.

A nasa jawabin Sarkin Maskan Katsina Hakimin Funtua Alhaji Sambo Idris Sambo ya yaba wa kwamishinan bisa tunanin da yayi na tallafa wa yara marayu da hakan zai ƙarfafa masu zuwa makaranta.

Hakimin ya kuma yabawa Hon Musa Adamu Funtua bisa ƙoƙarin da yayi wajen kawo na’urar shaƙar iska a babban asibitin Funtua da sauran muhimman abubuwan cigaba da kwamishinan ya kawo yankin.

By ukarofi