Masarutar Kontagora ta yi sabon sarki

Daga BASHIR ISAH

Kawo yanzu, Masarautar Kontagora a jihar Neja ta samu sabon sarki da zai ci gaba da jan ragamar harkokinta.

Muhammadu Barau Mu’azu shi ne wanda aka zaɓa daga jerin waɗanda suka nuna sha’awarsu ta zama sarki a matsayin magajin marigayi Alhaji Sa’idu Namaska.

MANHAJA ta kalato cewa Muhammadu Barau Muazu babban ɗan kasuwa ne kuma jikan Sarkin Sudan na 5, wato Alhaji Muazu Ibrahim, wanda ya yi mulki daga 1961 zuwa 1974.

An zaɓi Muhammadu Barau Muazu a matsayin sabon Sarkin Kontagora ne biyo bayan rasuwar tsohon sarki Sa’idu Namaska bayan da ya shafe shekara 47 kan kujerar sarauta, wato 1974 zuwa 2021.

A ranar Lahadin da ta gabata masu zaɓen sarki su biyar, suka zaɓi Muhammadu Barau Muazu a matsayin sarki na 7 na masarautar.

Waɗanda suka zaɓi sabon sarkin su ne: Alh. Aminu Ahmed Bawa (Madawaki), Alh. Shehu Yusuf (Galadima), Alh. Yusuf Tanko Usman (Waziri), Alh Adamu Moh’d Kanta (Magayaki) da kuma Alh. Abdulkadir Bashar (Kofa).