Daga CMG HAUSA
Mataimakin firaministan ƙasar Sin Hu Chunhua, ya jaddada muhimmancin wanzar da nasarorin yaƙi da fatara, tare da buƙatar ingiza raya yankunan karkara daga dukkanin fannoni, domin tabbatar da cewa, akasarin alummun da aka tsame daga kangin talauci ba su sake komawa ba.
Hu, wanda mamba ne a hukumar siyasa ta kwamitin ƙolin JKS, ya yi wannan tsokaci ne, yayin ziyarar aiki da ya gudanar a jihar Tibet mai cin gashin kanta tsakanin ranekun 1 zuwa 4 ga watan nan na Yuli.
Mataimakin firaministan ya ganewa idanunsa yadda alamura ke gudana a fannonin ayyukan yi, da sakamkon fitar da alumma daga ƙangin talauci, da ci gaban noma mai halayyar musamman ta yankin, da ayyukan samar da ababen more rayuwa a ƙauyuka, da sauran hidimomin kyautata rayuwar alumma da ake gudanarwa a jihar.
Hu ya ce ya kamata ƙarfafa matakan yaki da fatara su zamo kan gaba a dukkanin sassa da aka cimma nasarori, don haka ya yi kira da a ci gaba da ƙara azama, wajen samar da damar ƙara kuɗaɗen shigar alumma, ta hanyar inganta noma da kiwon dabbobi, da bunƙasa sarrafawa, da yada amfanin gona zuwa kasuwanni, da faɗaɗa sashen yawon bude ido na ƙauyuka da dai sauran su.
Mai Fassarawa: Saminu Alhassan
