Kyautata dangantaka da Sin na iya taimaka wa Amurka shawo kan matsalar tattalin arzikin

Spread the love

Daga FAEZA MUSTAPHA

Da safiyar yau Talata ne mataimakin firaministan Sin Liu He da sakatariyar baitulmalin Amurka Janet Yellen suka tattauna bisa gayyatar jami’ar ta Amurka.

Cikin batutuwan da Jami’an biyu suka tattauna, akwai na samar da daidaito a fannin sarrafa hajoji da shigar da su kasuwanni da farfaɗo da tattalin arzikin duniya. Dukkan ƙasashen biyu na da fasahohi da dabaru daban-daban da za su amfani juna. Ƙasar Sin a nata ɓangare, ta fi samar da kayayyaki masu rahusa, kana ta yi suna a duniya, wajen ƙerawa da sarrafa kayayyaki. A don haka, ’yan kasuwar Amurka za su iya amfana daga ɗimbin basirarta. A nata ɓangare, Amurka za ta iya amfana da manufar buɗe ƙofa ta ƙasar Sin, har ma da babbar kasuwar da ƙasar ke da ita.

Sin ta sha nanata cewa ƙofarta a buɗe take ga ’yan kasuwar ƙasa da ƙasa, haka kuma a kodayaushe, tana faɗaɗa buɗe ƙofar da rage yawan jerin ɓangarorin da kamfanonin waje ba za su iya zubawa jari ba, hakan ne ya sa ake ci gaba da ganin ƙaruwar jarin ƙasashen waje a ƙasar. Haka kuma, bisa tubali mai ƙarfi da tattalin arzikinta ke da shi, kamfanonin Amurka za su iya amfana sosai fiye ma da idan suka tsaya a ƙasarsu, muddun suka kiyaye dokoki da ka’idojin ƙasar Sin.

A matsayinsu na manyan ƙasashe, akwai ɗimbin abubuwan da za su iya amfana da su daga juna, muddin Amurka ta ajiye girman kai da cin zali. A halin yanzu, ana fuskantar hauhawar farashin kayayyaki da matsalar tattalin arziki mafi muni a Amurka, haɗin gwiwa da koyon dabarun ƙasar Sin, za su taimaka mata wajen shawo kan matsalar.

Idan ba a manta ba, Amurka ce ta fara kakkaɓa haraji kan wasu kayyakin Sin dake shiga ƙasar da fakewa da manufar tsaron ƙasa wajen hana kamfanoninta mu’amala da wasu daga cikin kamfanonin Sin, har ma an ga yadda a baya-bayan nan, ta zartas da dokar da ta gindaya sharuɗɗa kan audugar jihar Xinjiang. Sai dai dukkan wannan bai sa tattalin arzikin Sin ya durƙushe ba, sai ma kara samun tagomashi.

Wannan manuniya ce dake cewa, ya kamata Amurka ta yi karatun ta nutsu ta duba moriyarta da na al’ummarta, ta haɗa hannu da Sin domin a gudu tare a tsira tare domin amfanawa al’ummunsu da ma farfaɗo da tattalin arzikin duniya baki ɗaya.

Fassarawar: Faeza Mustapha

By Editor