Yadda za ka gane budurwarka yaudarar ka ta ke yi

Spread the love

Daga AMINA YUSUF ALI

Barkan mu da sake haɗuwa a wani makon cikin jaridarku mai farin jini ta Blueprint Manhaja. A wannan mako mun zo mu ku da yadda namiji zai gano cewa, budurwar da ya ke tare da ita yaudarar sa ta ke yi. Ya kamata mu sani, ba wai maza ne kawai suke yaudarar mata ba. Su ma matan akwai su da yawa mayaudara waɗanda suke soyayya da namiji ba don suna son sa tsakani da Allah ba, sai dai don yaudara.

To me ya sa ba sa rabuwa da waɗannan samari tunda ba son su suke yi ba? Amsar dai ba ta wuce kasancewar suna amfanuwa ta wata hanya da alaƙarsu da waɗancan samari nasu. Ko suna samun kuɗi ko alfarma a wajensu. Ko kuma suna kare yawa da su. Wato kada a gan su ba su da kowa da yake zuwa wajensu. Sai su riƙe saurayi guda su yi ta yaudarar sa duk da sun san ba shi ne irin namijin da suke ganin za su iya aura ba. Amma suna tare da shi ne suna ta yaudararsa yayin da suke jiran irin namijin da suke so ya zo. Sai dai ranar da ta samu ra’ayinta sai ta yanke ka a sabga.

Don ba kowacce mace ce ke iya fitowa fili ta nuna da ma ba sonka take yi ba. Musamman idan da ma can ta riga ta nuna maka son amma na yaudara. Ka ga a nan ba za ta iya fitowa fili ta gaya maka ba ta sonka ba sai dai ta cigaba da yaudararka a haka sai dai ka ji an ɗaura mata aure ko kuma ta ce maka auren dole iyayenta suka yi mata. Wasu matan ma don ƙwarewa a wajen wasan kwaikwayo har kuka za ta yi maka wai ita ba ta son wanda aka ba ta. Kai kuma gara sai ka yi ta rarrashi ba tare da ka san wasan kwaikwayo ne kawai ba.

Musamman matan da suka san sun ci kuɗin saurayi sosai kuma ba su da yadda za su amayar da shi idan ya buƙaci a biya shi. Wasu iyayen ma su suke shirya wa yaransu mata dabarar yadda za ta yi ta sallami saurayin da suka san tun farkon fari da ma ba aurensa za ta yi ba.

Shi ya sa wannan fili na zamantakewa a wannan mako ya kawo wa maza hanyoyin da za su farga su gano mayaudaran mata ba sai lokaci ya ƙure musu ba. Ba wai kuma su karanta ba kawai, su yi amfani da abinda suka karanta. Idan ba haka ba, garin kallon ruwa ba za su san lokacin da kwaɗo zai musu ƙafa ba. Sai a bi a hankali kada ka zama gara. Ta yi ta gara ka ita da ƙawayenta ko saurayinta kuma su kuma gefe su yi ta tsuntsura maka dariya a kan wautar da kake nunawa. Ga dai alamomin kada na ja mai karatu da surutu:

*Alama ta farko ita ce, za ka ga ba ta jin kunyarsa sosai. Komai tana iya yi a gabanka. Da ma dai akwai mata marasa kunya a Duniya, ba su nake magana ba. Amma galibi mace idan tana son mutum takan ji kunyarsa. 

*Rashin jin tausayinka. Tausayi dai yana daga alamar so. In dai saurayi ko budurwa ba sa tausayin wanda suke soyayya to wallahi a bincika akwai lauje cikin naɗi. Don haka a hankalta.

*Yawan roƙonsa alama ce da take nuna ba a sonka abin hannunka kawai ake so. Kuma idan ba ta samun abinda ta nema a wajenka, za ta iya canza ka duk wahalar da ka sha kuwa a kanta. Sannan idan ta samu wanda ya fi ka kuɗi za ta iya rabuwa da kai. Don haka, kada ka zama gara. A wanke ka a ƙara gaba a bar ka da cizon yatsa. 

*Ba ta son ka zo gidansu ko ka haɗu da iyayenta, musamman mahaifinta. Wata da ma bakinsu ɗaya da uwarta. Za ta haɗa kai da uwar su yi ta yaudararka.

*Ba ta iya kashe ko sisi a kanka. Kamar a ce ta saya maka wani abu don kawai tana ganin asarar ce.

*Ba ta kiranka ko ta neme ka idan ba kai ka neme ta ba. Sai dai idan tana buƙatar ɗaukinka. 

*Saurin fushi da gaba da kai ta yi ta gara ka ko da kuwa laifin bai kai ya kawo ba. Masoya musamman kafin su yi aure sukan yi wa juna uzuri sosai da kau da kai a kan laifinsu. Wani ma ko ya aikata za ta dage a kan ba haka ba ne. Amma idan ka ga tana ta wahalar da kai a kan laifin da bai kai ya kawo ba, to ba son. 

*Rashin nuna damuwarta da kai. 

  • Wulaƙanta ka a gaban mutane. 

*Rashin girmama ka.

*Nuna cewa idan za ka zo gidansu sai ka sanar da ita. Har fushi take yi idan ka yi mata zuwan ba-zata. 

*Yawan tara wasu samarin duk da ta yi maka alƙawarin za ta aure ka. 

*Yi maka qarya da zagaye-zagaye da suke nuna tana ɓoye maka abubuwa.

To idan tana maka waɗannan abubuwa ka cigaba da naci, to wallahi ka zama gara na gaske. Domin duk nacinka burinka ba zai cika ba na aurenta, sai dai ikon Allah. Idan mace tana son namiji ita ke bibiyarsa ko da ba ya kula ta. Idan kuwa ta ce ba ta sonka wallahi nacinka ba abinda zai ƙara, ba lallai ya sa ta so ka ba. To maza sai a yi karatu.

Me zai faru bayan mace mayaudariya ta gama zare zaren? 

Daga lokacin da amfaninka ya ƙare a wajen mayaudariyar budurwa ko bazawara, ko kuma ta samu wanda ya fi ka, ko kuma lokacin aurenta ya ƙara to, sai ta shiga sabuwar dirama ta rabuwa da kai ba tare da laifin yaudara ya hau kanta ba. Ga wasu hanyoyi da suke bi:

*Za ta fara yin abubuwanta ba tare da shawara da kai ba, sai dai kawai ka ji labari. 

*Za ta daina son ku haɗu. Idan ka yi magana ta yi ta kawo maka uzuri. 

*Idan a tana kiranka a da ko da saboda yaudara ne ko buƙatar ta, yanzu sam za ta daina ma kwata-kwata.

*Yanzu kullum musu kuke da cacar baki. Magana kaɗan, sai ta hayayyaqo maka ku haura. Ita dai birninta ku yi baram-baram ka daina ma neman ta, ita kuma sai ta samu ‘yancin rabuwa da kai. 

*Za ka ga ta cikin rashin nishaɗi da sakin fuska idan kuna tare. Kuma duk yadda ka tambaye ta ba za ta gaya maka dalili ba. 

*Kai a jikin ka ma za ka ji anya tana jin daɗin alƙarku? Gaskiya idan kai ba gara ba ne kamar yadda ta ɗauke ka ba, to ya kamata a ce ka kai gano. 

*Rashin ba ka muhimmanci kamar yadda take ba ka a baya. 

*Ta daina yi maka zance da magana kamar yadda take yi maka a baya. Ko hira kake yi mata ba ta mai da hankali sosai a kanka.

*Ba ta son ku dinga haɗuwa ko waya kamar a da can baya. Idan ka ce za ka zo sai ta dinga yi maka hanya-hanya har sai ka haƙura. 

*Za ta dinga ƙorafi a kan abubuwan da ba ta yi da a can baya. Kamar ta dinga cewa, ba ka iya kalaman soyayya ba, da sauransu. Komai ƙanƙantar abu sai ta nuna laifinka ne kuma ko ka yi bayani ta ƙi fahimta da gan-gan. Kuma ko tana da laifi ta ƙi karɓa. Ita dai dole sai an rabu dutse a hannun riga. 

*Ɓata maka suna a wajen iyayenta da sauran mutane don a ce kai ba mutumin kirki ba ne shi ya sa take so a rabu. 

*Idan kun yi alƙawarin aure a baya, za ta daina son zance gabaɗaya. Ko ɗauko zancen auren naku ka yi za ta kauce ta ƙi zancen. 

*Ta daina shakkar yi maka zancen wasu samarin ta da yin waya da su a gabanka . Ko da wajen ta ka zo, za ta iya barinka a tsaye ta je wajensa ita dai burinta ka harzuƙa ka yi zuciya ka rabu da ita ta samu ‘yanci. Wani lokacin ma har faɗa maka za ta yi kai tsaye, idan ba za ka iya ba ka rabu da ita mana. 

Me ya kamata saurayi/bazawari ya yi a wannnan yanayi mai wahala?

Na san wani saboda cda soyayya ya iya cewa bari ya cigaba da kula ta tare da fatan za ta gyara a gaba. Kar ka yi kuskure, yayana. 

Idan mace ta tayar da ƙayar baya, sai ta rabu da kai, duk da dai akwai ciwo, don Allah ka cika mata burinta ka rabu da ita ɗin. Domin duk tsananin nacinka ba dole ta amince maka ba. Ba riba a naci a kan abinda ba ka da tabbacin samu. Sannan ga mutuncinka da zai zube. Ko da ka same ta ɗin ma wataƙila sai ka ce sai ka fanshe wulaƙancin da ta yi maka. Ka ga ba kai ba sauran jin daɗi duk da ka same ta. Ka daure ka ƙara gaba kada ka zama gara mai nacin tsiya. Allah zai iya dubanka ya kawo maka mafita. 

Hakazalika, wataƙila sanadin rabuwar ma za ta iya kasancewa a gaba idan Allah ya sa rabonka ce, ku sake haɗuwa ku ƙara shiryawa. Idan an yi baram-baram a baya kuwa, an rufe ƙofar wannan sasancin.  

Amma idan kuma ka ga da damar sasantawa ne, za ka iya zaunar da ita ku fahimci juna. Sai dai abin da wuta. Allah dai ya sa mu dace. A nan za ku tsaya sai wani makon idan Allah ya kai rai.

By Editor