Matatar Dangote ta sake zaftare farashin fetur

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Matatar Man Fetur ta Dangote ta sake rage N10 akan farashin man fetur, inda ta rage daga N835 a hukumance zuwa N825 kan kowace lita.

Wasu majiyoyin da ke da masaniya kan lamarin sun bayyana a ranar Litinin cewa, tun da farko, ‘yan kasuwar sun biya Matatar Naira 835 kan kowacce lita amma daga baya, sai aka mayar musu da ragin Naira 10 bayan sun yi dakon man daga matatar.

Wata majiya ta tabbatar da cewa, “matatar man Dangote ta fara bayar da rangwame kan kayayyakin da take samarwa, babu sanarwa a hukumance, amma an tura wa ‘yan kasuwar da rangwamen a asusun su bayan sun fitar da man daga Matatar.”

Wannan rangwamen farashin duk da cewa ba a hukumance yake ba, amma ya bai wa kwastomomin Dangote damar siyar da mai akan farashi mai rahusa a tsakanin N830 zuwa N835 kan kowacce lita.

Wannan nasarar ta zo ne makonni kadan bayan da matatar ta yi ragin farashi sau biyu a jere a cikin mako guda a cikin watan Afrilu, inda ta rage farashin man ta daga N880 zuwa N835 kan kowace lita.

Ana kyautata zaton cewa, ragin na da nasaba da sabunta tsarin sayen ɗanyen mai da takardar Naira, biyo bayan dakatarwar da aka yi na wucin gadi.

By ukarofi