Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Matatar man fetur ta Dangote ta sanar da shirin riƙa samar da litar fetur biliyan 1.5 kowane wata ga kasuwar Nijeriya daga watan Disamba 2025 zuwa Janairu 2026, domin tabbatar da wadataccen mai ba tare da tangarɗa ba a lokacin bukukuwan Kirsimeti da shiga sabuwar shekara.
Shugaban rukunin kamfanin Dangote kuma Shugaba na Matatar Dangote, Alhaji Aliko Dangote ne ya bayyana wannan shiri a ƙarshen mako.
Ya ce, matatar za ta fara sakin litar fetur miliyan 50 a kullum tun daga ranar 1 ga Disamba.
A cewarsa, wannan shiri na samar da biliyan 1.5 na fetur a cikin wata guda daidai yake da litar miliyan 50 a rana.
Ya ce, an riga an sanar da Hukumar Kula da Haƙowa da Tace Man Fetur a hukumance game da wannan alƙawari.
Ya ƙara da cewa, a watan Janairu ma za a ci gaba da samar da adadin biliyan 1.5, yayin da a watan Fabrairu kuma za a ƙara zuwa biliyan 1.75, wanda ke nufin sama da lita miliyan 60 a kullum.
Alhaji Dangote ya bayyana hakan ne a lokacin wata ziyarar da jami’an South-South Development Commission suka kai wa matatar tare da rukunin masana’antar taki ta Dangote.
Ya ce, a halin yanzu matatar na da isasshen ajiyar mai kuma tana samar da tsakanin litar miliyan 40 zuwa 45 na fetur a kullum.
Ya ce, wannan mataki zai kawar da shakku da ake yawan yi cewa matatun cikin gida ba su da ƙarfin biyan buƙatar man fetur ta ƙasa.
A cewarsa, kamfanin na ci gaba da tattaunawa da ‘yan kasuwar man fetur domin ƙarfafa hanyoyin rarrabawa, ciki har da amfani da motocin ɗɗukar mai masu aiki da iskar gas.
“Abin da muka sa a gaba shi ne tabbatar da Nijeriya ta samu isasshen mai. Wannan ba wai don riba ba ne, sai domin kare lafiyar tattalin arzikin ƙasa da rayuwar al’umma. Wannan shi ne irin juyin juya halin da muka haifar a fannin siminti,” inji Dangote.
A wata wasiƙa da Daraktan zartarwa na Matatar Dangote, David Bird, ya sanyawa hannu zuwa ga shugaban hukumar NMDPRA, kamfanin ya gayyaci hukumar da ta aike da jami’anta domin su duba da idonsu yawan man da ake samarwa a kullum, domin ƙaryata raɗe-raɗin da ake yaɗawa.
Kamfanin ya ce, a shirye yake ya wallafa a kafafen yaɗa labarai na intanet da jaridu adadin man da yake samarwa da ajiyar da yake da shi a kullum, domin nuna cikakken gaskiya da riƙo.
Dangote ya kuma bayyana cewa ana ci gaba da shirin faɗaɗa matatar zuwa ta kai ƙarfin samar da gangar mai miliyan 1.4 a rana. Ya ce fiye da ma’aikata 100,000 ake sa ran za su samu aiki a lokacin faɗaɗa matatar da masana’antar taki baki ɗaya.
A nata jawabin, Babbar Darakta a SSDC, Usoro Offiong Akpabio, ta yaba wa Dangote bisa rawar da yake takawa wajen ƙarfafa masana’antu, tabbatar da tsaron makamashi da kuma bunƙasar tattalin arzikin Nijeriya na dogon lokaci.
Ta bayyana yankin Kudu maso Kudu a matsayin cibiyar makamashi ta ƙasa, mai yawan arzikin ɗanyen mai, gas, tashoshin ruwa da harkokin noma da masana’antu.
Ta ce, zurfafa haɗin gwiwa tsakanin yankin da kamfanin Dangote zai buɗe damar zuba jari a rarraba kayayyaki, iskar gas, sinadaran petrochemical, noma da samar da ayyukan yi.
Ta ƙara da cewa, irin wannan haɗin gwiwa zai taimaka wa shirin gwamnatin tarayya na tabbatar da kwanciyar hankali a fannin makamashi tare da mayar da yankin cibiyar bunƙasar kasuwanci ga rukunin Dangote.
