Muna kira ga gwamnan Kano da ka da ya koma APC – Dungurawa

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Shugaban Jam’iyyar NNPP na jihar Kano, Hon. Suleiman Hashim Dungurawa ya ce gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da duk waɗanda za su bi shi zuwa jam’iyyar APC sun yi hakan ne domin raɗin kansu sannan sun yi iya yinsu wajen ganin ba su ɗauki matakin sauya sheƙar ba.

“Ina so na sanar cewa da jam’iyya ta Kano, da kasa da Jagora na Kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwasiyya da sauran jagorori duk abin da yake faruwa ba da lamuncewarmu ba ne. Hasali ma, duk abin da za mu iya mun yi don su yi hakuri kar su koma APC saboda hakkinmu da ke kansu, da kuma hakkin jama’ar Kano amma abubuwa sun ci tura,” inji Suleiman Hashin.

Sai dai kuma shugaban jam’iyyar ta NNPP a Kano ya roƙi gwamnan da ya mayar da wuƙarsa kube.

“A madadinmu gaba ki ɗaya, muna sake roƙonsu da su yi wa Allah su yi wa Annabi ka da su bar wannan jam’iyyar kar su bar wannan jam’iyya su koma wadda aka yi hamayya da ita kuma talakawa da sauran masu zabe suka ka da ita.”

Daga ƙarshe Suleman Hashimu ya tabbatar wa da jama’a cewa shi da wasu jiga-jigan ‘yan jam’iyyar da ake ta yaɗa jita-jitar cewa su ne suka haɗa gwamna Abba da Kwankwaso ba gaskiya ba ne.

“Ina son na jawo hankalin masu yadda jita-jita cewa, musamman akwai wasu da suke hada Gwamna da Jagora Sanata Kwankwaso; musamman mataimakin gwamna, da Sanusi Surajo da Hashimu Dungurawa da Sanata Rufai Hanga, ana ganin ana zargin mu saboda ganin kusancinmu da jagora, amma mu ba mu taba hada kowa da jagora ba, amma idan wani yana da shaida sai ya fito da ita, kuma Allah ya ba su hakuri.”

By ukarofi