‘Mutum 600 da suka ɓace a ambaliyar Mokwa sun mutu’

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

’Yan Majalisar Wakilai daga jihohin Neja da Kwara sun shaida wa majalisar cewa mutum 600 da suka ɓace a ambaliyar garin Mokwa kuma har yanzu ba a gan su ba, za a ɗauka su ma sun mutu.

ɗan majalisa Joshua Audu Gana (Neja) da Saba Ahmed Umaru (Kwara) ne suka bayyana hakan a yayin gabatar da wani ƙudurin gaggawa a zauren majalisar a ranar Laraba.

Sun ce mummunar ambaliyar da aka yi a ranakun 28 da 29 ga watan Mayun da ya gabata sanadin mamakon ruwan saman da aka tafka ta yi barna sosai a ƙaramar hukumar ta Mokwa a jihar Neja, sannan ta tsallaka har ƙaramar hukumar Edu ta jihar Kwara.

A cewar ’yan majalisar, yayin da aka tabbatar da mutuwar mutum 500, su kuma ragowar sama da 600 da aka ce sun ɓace kuma har yanzu babu labarinsu, su ma za a ƙirga su a cikin matattun, la’akari da munin ambaliyar.

’Yan majalisar sun kuma ce ambaliyar ta lalata gidaje sama da 4,000, ta jikkata sama da mutum 200, sannan ta shanye gonaki da gine-gine, ta kuma raba dubban mutane da muhallansu.

Daga nan ne majalisar ta yi shiru na minti ɗaya don girmama waɗanda ambaliyar ta shafa, sannan ta yaba wa Shugaban ƙasa Bola Tinubu saboda amincewa a bayar da tallafin Naira biliyan biyu ga waɗanda lamarin ya shafa.

Majalisar, bayan tafka muhawara, ta kuma amince da ƙudurin sannan ta ba da umarnin inganta matakan daƙile ambaliya a yankin da ma sauran yankunan da ke cikin barazanar ambaliyar, cikin gaggawa.

Kazalika, majalisar ta kuma umarci Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta ƙasa (NEMA) da ta samar da kayayyakin agaji da na tsafta ga al’ummomin da lamarin ya shafa domin kaucewa sake ɓarkewar cututtuka.

By ukarofi