Nan ba da daɗewa ba ƙarin gwamnoni da ‘yan majalisar dokoki za su koma APC – Yilwatda 

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, ya bayyana cewa nan ba da daɗewa ba wasu gwamnonin jihohi da ‘yan majalisar dokoki za su koma jam’iyya mai mulki gabanin babban zaɓen 2027.

Mista Yilwatda ya bayyana hakan ne yayin taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC karo na 12 a jihar Bayelsa.

A cewarsa, sauya sheƙar za ta ƙarfafa wa Shugaba Bola Tinubu karagar mulki a karo na biyu a 2027.

Shugaban wanda mataimakin shugaban jam’iyyar na ƙasa (Kudu) ya wakilta, Emma Eneukwu, ya ce ayyukan Mista Tinubu a harkokin mulki na janyo hankalin gwamnoni, da Sanatoci, da sauran manyan ‘yan siyasa daga jam’iyyun adawa.

“Har yanzu ƙarin gwamnoni da ‘yan majalisa suna kan hanyarsu ta zuwa jam’iyyarmu saboda mutunci, da kuma nasarorin da shugaban ƙasa ya samu.

“ƙofofinmu a buɗe suke don karɓar waɗanda ke son haɗa hannu da mu don ciyar da Nijeriya gaba.”

A cewarsa, ficewar da gwamnan jihar Delta, Sheriff Oboreɓwori, gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Eno, ya yi a kwanakin baya daga PDP zuwa APC, wata alama ce da ke nuna irin tasirin da shugaban ke da shi.

Mista Yilwatda ya buƙaci ‘ya’yan jam’iyyar a Bayelsa da su kasance da haɗin kai domin ganin an samu gagarumar nasara a 2027.

“Sauran jam’iyyun na iya yin surutu, amma idan kana da zaki, ba ya damu da kare kare – yana mai da hankali kan manufarsa, abin da Shugaba Tinubu yake yi kenan ɗaukar bijimin da kaho inda wasu ba su da ra’ayin siyasa,” inji shi.

Ya ƙara da cewa yankin Kudu maso Kudu ya nuna karamci a siyasance ta hanyar haɗa kai da jam’iyyar APC, inda ya ce gwamnonin yankin sun yi watsi da tsofaffin jam’iyyunsu domin goyon bayan manufar shugaban ƙasa.

“Daga Kudu maso Kudu zuwa Kudu maso Gabas, shugabanni suna yanke hukunci na gaskiya, suna barin jam’iyyunsu ne domin su marawa shugaban ƙasa baya saboda sun ga aniyarsa ta kai Nijeriya ga wani matsayi mai girma,” inji shi.

By ukarofi