Nasarata a Gasar Tsangayar Gusau ce ta ba ni lasisin amsa sunan marubuciya  – Ummi Abba

Spread the love

“Ko yau na ajiye alƙalami zan iya cewa kwalliya ta biya kuɗin sabulu”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU 

Akwai marubutan Hausa da dama dake bayar da gudunmawa sosai ga cigaban rubutun Adabi, sai dai ba kasafai ka ke jin amon su daga Jihar Borno ba, duk kuwa da kasancewar akwai marubuta da dama da suka shahara daga wannan yankin. Fatima Abba Muhammad, ba sunanta ne kawai ya bayyana ba, ta kasance ma a cikin gwarazan da suka yi fice a Gasar Tsangayar Gusau, ɗaya daga cikin manyan gasannin marubutan Hausa da ake sa su a Arewacin Nijeriya, inda ta samu nasara a shekarar 2024. Marubuciyar ta shaidawa wakilinmu Abba Abubakar Yakubu cewa, tun tana ƙarama ta taso da burin zama marubuciya kuma malamar makaranta. Idan kun nitsa cikin tattaunawar tasu za ku ji irin nasarorin da ta samu da yadda ta samu gogewa akan sanin dabarun rubutun labari da ƙa’idojin rubutu. 

MANHAJA: Ki gabatar mana da kanki.

UMMI: Sunana Ummi Abba Muhammad, amma an fi kira na da Ummulkhairi. Ni marubuciya ce, kuma malamar makaranta. Ni asalin ƴar Jihar Borno ce daga Maiduguri.

Ki ba mu tarihin rayuwarki da matakin da ki ke na karatu.

An haife ni a tsakiyar birnin Maiduguri a unguwar Mafoni. Na yi karatuna na firamare da sakandire duk a Maiduguri, sai bayan na kammala ne na wuce Kwalejin Nazarin Dokokin Shari’ar Musulunci ta Muhammad Goni College of Legal and Islamic studies, inda na yi karatu a ɓangaren koyon aikin malanta. Na samu shaidar karatun NCE a ɓangaren Larabci da Ilimin Musulunci. Bayan na kammala ne sai na fara koyarwa a wata makaranta mai zaman kanta dake nan cikin Maiduguri. Ina cikin aikin koyarwa na samu gurbin karatu a Jami’ar Maiduguri domin samun gogewa kan layin da nake na koyarwa. Na samu digirina na farko a ɓangaren koyar da harshen Larabci. A yanzu haka, cikin yardar Allah ni malama ce a wata makarantar ƙaramar sakandire ta gwamnati. 

Ba mu labarin yadda ƙuruciyarki ta kasance, wacce tarbiyya ki ka samu yayin tasowarki?

ƙuruciyata ta kasance cikin neman ilimi ne, wato zuwa makaranta a kullum. Idan an dawo gida kuma na taya mahaifiyata ayyukan gida. Tarbiyya kuma, Alhamdulillahi. Iyayena sun yi ƙoƙari wajen ba mu tarbiyyani da sauran ƴan’uwna, ina kuma roƙon Allah mu ma Ya ba mu ikon tarbiyyartar da namu idan Allah Ya bayar gwargwaɗon iko.

Wanne buri ki ka taso da shi a rayuwarki?

Duk da za ka samu mafi akasarin mutane ba su son aikin koyarwa, amma ni na taso da burin son koyarwa, kuma kasancewata ma’abociyar son karance-karance sai na ji ina ƙwaɗayin son zama marubuciya.

Yaya aka yi ki ka fara sha’awar rubuce-rubuce?

Na fara sha’awar rubuce-rubuce ne dalilin karance-karance da nake yi, ina cewa a raina ni ma ina so in samu damar bayar da gudunmawa a fannin rubutu.

Wane ne ya fara koya miki yadda ake rubutun adabi?

Gaskiya ba zan iya ce koya mini rubutu aka yi ba, akwai dai littattafai da na riƙa karantawa a baya, wanda marubuci Kabir Yusuf Fagge (Anka) ya ba ni shawara da na saye su za su taimaka mini matuƙa a harkar rubutu, kuma babu shakka na ji daɗinsu sosai. Littattafan su ne, ƙa’idojin Rubutun Hausa, Matashiya Ga Marubuta, da Ilimin Rubutun Labari Cikin Adabi. Na saye su kuma na yi nazarinsu sosai, na ji daɗin littattafan don sun taimaka mini matuƙa. Hakazalika kasancewata a zaurukan marubuta shi ma ya taimaka mini sosai don ina ƙaruwa da abubuwa da dama. To, zan iya cewa ta waɗannan hanyoyi ne na koyi yadda ake rubutun adabi.

Kawo yanzu kin rubuta cikakken littafi guda nawa? Gajerun labarai nawa? Za ki gaya mana sunayen su?

Bari na fara da maganar malamin mu, kafin na kai ga ba da wannan amsar tambayar, Malam Jibril Adamu Rano (Abu Amra) ya ce nagartar marubuci ba daga yawan littattafan da ya yi ba ne. To, a gaskiya nima ban yi wasu littattafai da yawa ba, cikakkun littattafai huɗu kawai na rubuta. Su ne, ‘Silar Kafar Sadarwa,’ ‘Su Ma ‘Ya’ya Ne,’ ‘Mijin Mace ɗaya,’ da kuma, ‘Abin Da Ka Shuka…’ wanda na samu nasarar cin Gasar Tsangayar Gusau da shi.

Gajerun labarai kuma a gaskiya suna ɗan dama, nemo su da kirga su zai ba ni wahala, don ni tun ban san komai a harkar rubutu ma nake da karambanin fara rubutun shiga gasa, har zuwa gasar Hikayata ta BBC Hausa.

Ki yi mana bitar littattafanki uku da suka yi fice.

Littafin ‘Su Ma ‘Ya’ya Ne,’ yana ɗaya daga cikin littattafaina da suka samu karɓuwa sosai, don masu karatu sun yi mini sharhi da tsokaci akai, wasu ma har kai tsaye suke min magana da bayyana jin daɗinsu da yi min addu’o’in fatan alheri. 

A labarin, Su Ma ‘Ya’ya Ne, Allah Ya jarabci tauraruwar labarin da irin maƙauniyar soyayyar nan. Mafi akasarin labarai akan ci karo da ma’aurata suna shan soyayya, sai dai ita wannan jarumar dududu soyayyar sati biyu kawai ta ɗanɗana a gidan aurenta kafin nan ta faɗa cikin tasku da ƙangin jarrabawa, a haka har ta haifi ‘ya’ya mata biyar.

Labari ne da na gina shi akan wani mahaifi wanda shi kuma ‘ya’ya maza yake so a haifa masa, amma sai Allah Ya jarabci matarsa da haihuwar ‘ya’ya mata. Wannan ne ya sa tsanar da yake mata ta ƙaru, ba ma ita kaɗai ba har da abin da ta haifa. Ya riƙa muzguna wa rayuwarsu, ya wofintar da uwar da ‘ya’yan, daga ƙarshe kuma ‘ya’ya matan ne suka kasance masu jinƙansa, yayin da duniya ta juya masa baya. Saƙon labarin dai yana nuna mutum ya roƙi Allah ya arzurta shi da ‘ya’ya masu albarka ba wai mace ko namiji ba.

Shi kuma littafin Mijin Mace ɗaya, yana ƙunshe ne da saƙon jan hankali dangane da mazan da tun kafin a kai ga aure giyar soyayya idan ta ɗebe su sukan yi wa matansu alƙawarin da ita ɗaya za su rayu ba za su ƙara aure ba, sun manta da ƙarin aure nufi ne na Allah, ko kana da wannan ƙudirin kar ka furta ka bari kawai a zuciyarka don ba ka san me Allah ya tsara maka a rayuwarka ba.

Sannan kuma akwai wani ɓangare a labarin yadda uwar miji ta sa matar ɗanta a gaba duk da kasancewarta mai biyayya a gare ta. Shi ma littafin ya samu karɓuwa babu laifi.

Sai littafin ‘Silar Kafar Sadarwa’, shi kuma ya kasance shi ne littafina na farko. Na rubuta shi ne a lokacin ban san komai ba game da abin da ya shafi rubutu, a lokacin ban ma sayi littattafan da Kabir Yusuf Fagge ya bani shawarar karantawa ba, kuma ba na cikin zaurukan da ake tura littattafai na onlayin. Lokacin da nake rubuta shi na riƙa ɗora wa ne a manhajar Wattpad, kuma cikin ikon Allah an samu mutane masu karantawa da yin sharhi a kai. Ina da burin yanzu haka na bibiyi labarin na yi masa gyara saboda yanzu na ɗan samu gogewa kaɗan fiye da lokacin da na yi shi. Saƙon labarin ya ƙunshi yadda ‘yan mata ke amfani da kafar sadarwa wajen bayyana hotunansu ba su san yin hakan na da matuƙar hatsari ba.

Wacce ƙungiyar marubuta ki ke, kuma wanne cigaba ta kawo a rayuwarki ta rubutu?

Ina ƙarƙashin ƙungiyar Young Talented Writers’ Association (YOTA) ne. Haƙiƙa ƙungiyata ta kawo mini cigaba sosai, don na samu ilimin da a baya na jahilce su a cikinta. Ina alfahari da ƙungiyata kuma ina yi mata fatan ɗaukaka da cigaba a kodayaushe.

Ba mu labarin yadda ki ka samu nasara a Gasar Tsangayar Gusau ta 2024? Wanne littafi ne ya baki nasara, kuma yaya jigonsa yake?

Nasarata a Gasar Tsangayar Gusau ta yi mini zuwan bazata, domin wannan gasar ita ta ba ni lasisin amsa sunan ni marubuciya ce ashe da gaske, don a baya gani nake shirme nake yi, kuma nakan ɓoye kaina. Sunan labarin da na yi nasara a gasar, kamar yadda na faɗa a baya shi ne, Abin Da Ka Shuka…Ya zo a matsayin mataki na biyu wato (Second Prize Winner), har yanzu ina furta kalmar Alhamdulillahi, bisa wannan nasara da na samu. 

Masu magana kan ce, kwaɗayi mabuɗin wahala. Son zuciya ɓacinta, da wannan karin maganar zan hasko jigon labarin na ce, jigo ne akan ƙwaɗayi da son zuciya. 

Sau nawa kika shiga wannan gasa ta Tsangayar Gusau?

Na shiga wannan gasa sau uku, kuma duk biyun ko zagayen farko labaran ba su taɓa tsallakawa ba. Tabbas haƙuri mai tadda rabo ne. 

Akwai masu cewa Gasar Gusau ba duk marubuci ne zai iya shigarta ba, me ya baki ƙwarin gwiwa ke ki ta shiga haka?

Gaskiya Gasar Tsangayar Gusau gasa ce mai matuƙar wahala ba ka gane alƙiblarsu, misali hikayata an daɗe da fahimtar inda suka dosa suna so a rubuta labari dangane da abin da ya shafi mata kamar ƙalubale da mata ke yawan fuskanta ko kuma abin da mace ta jawowa kanta, idan mutum ya girka labarinsa a salon da suke so idan da rabo sai ya dace. Amma ita Gasar Tsangayar Gusau mutum ba ya sanin takamaiman abin da suke so, an gaza fahimta. Duba da irin hakan ne ma shi ne wasu ke faɗin gasar na da wahala, baya ga haka shi littafi sukutum ne ba kamar sauran gasa ce da mafi akasari kalmomi 1500 ne kawai.

Abin da ya ba ni ƙwarin gwiwa shi ne; na yarda na kuma gaskanta, nasara da faɗuwa duk ɓangarori ne na gasa. Ba wanda ya taɓa kai wa ƙololuwa ba tare da ya taɓa tuntuɓe ba. Faɗuwa ba alamar rauni ba ce alamar ƙoƙari ce. Idan mutum bai gwada ba, ba zai taɓa faɗuwa ba, kuma ba zai taɓa yin nasara ba.

Na ɗauki kowacce faɗuwa a matsayin darasi, ba hukunci ba. Gasa ta daɗe da koya mini haƙuri, jajircewa, da yarda da kaina. Haka kuma wanda ya dage shi ke kai wa gaci. Nakan tuna:

Bayan wuya sai daɗi. Wanda ya yi haƙuri, shi ke cin riba.

Nasara ta gaskiya ita ce ka tashi duk lokacin da ka faɗi. Ka cigaba da ƙoƙari, ka yarda da kanka, ka ƙara zage damtse sai ka sake gwadawa. Ranar da za ka yi nasara za ta zo kuma lokacin nan za ka gane cewa duk faɗuwar da ka yi matakala ce ta kai ka can.

Ban da Gasar Tsangayar Gusau kin taɓa shiga wata gasar marubuta? Wacce nasara ki ka samu da wanne labarin?

E, ina shiga wasu gasanni amma ba kowanne ba, sai wadda na gamsu da ita.

Samun nasarar zama gwarzuwa kam zan ce a Gasar Gusau Institute ne kawai.

Ki gaya mana sunan labarin, da ƙungiyar da ta shirya gasar, shekarar da aka yi, da kuma labarin da ki ka shigar a gasar?

 Na shiga Gasar Hikayata da BBC Hausa ke shiryawa. A shekarar 2025 labarina ya samu nasar fitowa cikin labarai 12 waɗanda suka cancanci yabo. Sunan labarin Zaɓi ɗaya.

Yaya ki ke ji game da waɗannan nasarori da ki ke samu a dalilin rubutu?

Ina kasancewa cikin farinciki da annashuwa, haka kuma ba na gajiya da yi wa Allah godiya domin yin shi ne bai ba. Kuma da gudunmawar manyan marubutan da suke duba mana labari su yi mana gyara. Ko yau na ajiye alƙalami zan iya cewa Alhamdulillah, kwalliya ta biya kuɗin sabulu. 

Kin taɓa samun wani ƙalubale a dalilin rubutu, ko saboda hulɗa da marubuta?

Ban taɓa fuskanta ba gaskiya.

Gaya mana marubutan da rubutun su yake burgeki a maza da mata?

Duk wani marubuci tun da Allah ya ba shi baiwar ƙirƙirar labari yana burge ni.

Akwai wacce ki ke kwaikwayon salon rubutunta a cikin marubuta?

Gaskiya babu, amma ina son labarin da aka zuba ruwan karin magana da azanci aka kuma ƙawata shi da adon harshe.

Idan za a ba ki dama wanne sauyi za ki kawo wa harkar rubutun Hausa?

Sauyin da zan kawo daƙile masu rubutun batsa, ka san an ce, wake ɗaya shi ke ɓata gari, don har ga Allah suna ɓata mana suna, waɗanda ba su fahimta ba suna yi ma duk wani marubuci kallon mai lalata tarbiyya da yaɗa alfasha, ba su san kowanne tsuntsu kukan gidansu yake yi ba.

Sannan kuma zan yi ƙoƙarin fito da marubuta a idon duniya, yanzu misali a fim, idan fim ya yi kyau sai dai a yabawa jarumin ko darakta ba a san marubucin da ya tsara labarin ba ne ya cancanci yabo.

Kamar yadda ake yin, Daga Bakin Mai Ita, da wasu shahararru zan samar da irin shirin ga marubuta ta wannan hanyar za a hasko rawar da suke takawa.

Wanne abu ne ya fi ɗaure miki kai a harkar rubutu?

Samar da sunan labari.

Da wanne lokaci ki ka fi jin daɗin yin rubutu? Kuma wanne yanayi ne ya fi kawo miki sauƙin ilhamar rubutu?

Kowanne lokaci zan iya rubutu muddin babu hayaniya a wurin da nake. Idan ina cikin shauƙin son yin rubutu a kowanne yanayi nakan samu ilhama, amma idan ba shauƙin sai ka ga babu wata hikima da za ta zo min.

Shin ban da rubutu wacce sana’a ko aiki ki ke yi, wacce aka fi saninki a kai?

Aikin koyarwa shi ne abin da aka fi sanina da shi. Ni Malama ce a makarantar ƙaramar sakandire ta gwamnati.

Wasu marubutan adabi suna komawa rubutun fim, shin ke ma kina da ra’ayin komawa rubutun fim?

Gaskiya ina da ra’ayi, idan har zan samu wannan damar ai cigaba ne.

Wanne launin kala ne ya fi burge ki?

Ruwan ƙasa-ƙasa (Brown).

Wacce karin magana ce take tasiri a rayuwarki?

Zakaran da Allah Ya nufa da cara, ko ana muzuru ana shaho sai ya yi.

Mun gode ƙwarai da samun damar amsa tambayoyin mu da ki ka yi.

Ni ma na gode.

By ukarofi