NCC ta umarci kamfanonin kiran waya su biya kwastomomi diyya bisa ɗaukewar sabis na sama da kwana ɗaya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Hukumar Sadarwa ta Ƙasa, NCC, ta yi aiken sabon umarni ga kamfanonin telekom da su riƙa biyan kwastomomi diyya a duk lokacin da aka samu ɗaukewar sabis na sama da sa’o’i 24.

A ranar Lahadi hukumar ta bayyana hakan a wata takarda, inda ta ce wajibi ne a biya diyya ga dukkan kwastomomin da irin hakan ya shafa gami da faɗaɗa wa’adin sabis bisa la’akari da kiyaye dokar bai wa kwastomomi kariya.

Sabuwar dokar ta shafi masu gudanar da harkokin sabis na wayoyin kira, masu samar da sabis na yanar gizo da kuma sauran masu isar da sabi ga kwastomomi a sassan ƙasar.

Haka kuma ta ce hakan wani mataki ne na inganta ƙarfin sabis da tabbatar da tsare gaskiya da adalci gami da kare ƴancin kwastomomin telekom a Nijeriya.

Ƙari akan haka, hukumar ta kuma buƙaci masu gudanar da harkokin telekom da su riƙa sanar da al’umma a duk lokacin da aka samu tsaiko game da abinda ya haddasa da wuraren da ya shafa da kuma wa’adin da zai ɗauka wajen shawo kansa.

Haka kuma, a sanar sati guda kafin faruwarsa ta kafafen sadarwa da suka dace.

Bugu da ƙari, a ƙoƙarinta na yin adalci, NCC ta ƙaddamar da babban shafin ruwaito tsaiko a ɓangaren wanda zai bada yalwataccen bayani game da ɗaukewar sabis da waɗanda ke da alhakin hakan musamman a yayin zagon-ƙasa.

Matakin ya yi daidai da umarnin Shugaba Bola Tinubu na gudanar da ɓangaren sadarwa cikin inganci, lamarin da kai-tsaye ya shafi harkokin tsaro da ɗorewar tattalin arziƙi.

By Babaji