Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Asusun Ba da Lamunin Karatu na ƙasa (NELFUND) ya fara wani babban nazari kan tsarin tafiyar da ayyukansa, domin ƙarfafa ginshiƙan hukumarsa, inganta yadda take gudanar da ayyuka da kuma shirya kanta domin faɗaɗa ayyukanta a nan gaba.
Asusun ya bayyana cewa manufar bitar ita ce tabbatar da cewa tsarin gudanarwarsa, hanyoyin aiki da matakan da yake bi sun dace da ƙarin buƙatun da ke tattare da aikinsa na samar da damar samun tallafin kuɗin karatu ga ɗaliban Nijeriya da suka cancanta.
Tun bayan fara shirin bayar da lamunin karatu ga ɗalibai, NELFUND ya taimaka wa kusan ɗalibai 870,000, tare da bayar da lamunin da ya haura naira biliyan 375. A cewar hukumar, wannan gagarumin ci gaba ya sa ya zama wajibi a ƙara ƙarfafa ƙarfinta na gudanarwa, domin ta iya ci gaba da tafiyar da ayyukanta yadda ya kamata.
A cikin wata sanarwa da Daraktar Sadarwa da Tsare-tsaren Hulɗa da Jama’a ta asusun, Oseyemi Oluwatuyi, ta fitar ranar Lahadi, NELFUND ya ce bitar za ta duba tsarin ayyukan da ake amfani da shi a halin yanzu, gano wuraren da ake buƙatar gyara da kuma gabatar da shawarwarin da za su taimaka wajen inganta ingancin gudanarwar hukumar. Ya ƙara da cewa, nazarin zai taimaka wajen fayyace nauyin da ke rataye a wuyan sassa da ma’aikata daban-daban, tare da inganta ayyukan da ake bayarwa ga ɗalibai da sauran masu cin gajiyar shirin.
NELFUND ya bayyana cewa ya ɗauki wani kamfanin ƙwararrun masu ba da shawara mai zaman kansa, wanda ke da ƙwarewa a fannin inganta tsarin ƙungiyoyi da sake fasalin hukumomin gwamnati, domin gudanar da aikin bitar. Asusun ya ce an gudanar da tsarin ɗaukar kamfanin ne bisa ƙa’idojin dokar sayen kayayyaki da ayyukan gwamnati ta shekarar 2007, da sauran dokoki da ƙa’idojin da suka dace. Ya bayyana cewa hakan na daga cikin ƙoƙarinsa na tabbatar da gaskiya, riƙon amana da kuma kula da dukiyar al’umma yadda ya kamata.
A cewar hukumar, kamfanin zai gudanar da aikin cikin ’yanci, ba tare da katsalandan ba, tare da gabatar da shawarwari bisa sahihan bayanai da hujjoji. NELFUND ya jaddada cewa kiyaye sahihancin wannan tsari na da matuƙar muhimmanci, domin tabbatar da cewa sakamakon bitar zai amfani hukumar baki ɗaya tare da ƙarfafa ayyukanta.
Hukumar ta kuma tabbatar wa ɗaliban da ke cin gajiyar shirin, manyan makarantu da sauran masu ruwa da tsaki cewa wannan bita ta shafi tsarin gudanarwar cikin gida ne kawai, kuma ba za ta kawo cikas ga ayyukanta na yau da kullum ba. Ta ce karɓa da tantance buƙatun neman lamuni, amincewa da bayar da lamuni, tura kuɗaɗen ga makarantu da sauran ayyukan da suka shafi shirin za su ci gaba ba tare da tangarɗa ba.
NELFUND ta bayyana cewa ƙarfafa ginshiƙan hukumarta na da muhimmanci wajen bunƙasa nasarorin da ta samu, magance sabbin ƙalubalen da ka iya tasowa da kuma ƙara faɗaɗa gudummawar da take bayarwa ga ɓangaren ilimin manyan makarantu a Nijeriya.
Sanarwar ta ce manufar ita ce gina hukuma mai ingantaccen tsari, ƙwarewa da ƙarfin gudanarwa wanda ya dace da girman nauyin da aka ɗora mata, da kuma irin tsammanin miliyoyin ɗaliban Nijeriya da take da burin yi wa hidima. Asusun ya sake jaddada aniyarsa ta gina hukuma mai ƙarfi kuma mai ɗorewa, wadda za ta iya faɗaɗa damar ɗalibai na samun lamunin karatu tare da inganta damar shiga manyan makarantu a faɗin ƙasar.
