Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta sanar da cimma wata babbar yarjejeniyar kasuwanci tsakanin Nijeriya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) wadda ta tanadi soke haraji kan fiye da kayayyaki 13,000 domin bunƙasa cinikayya tsakanin ƙasashen biyu da kuma haɓaka fitar da kayayyakin da ba na mai ba daga Nijeriya.
A cewar wata takarda da Ma’aikatar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari ta Tarayya ta fitar, Nijeriya ta soke haraji kan kayayyaki 6,243 da ake shigowa da su daga UAE, yayin da UAE ta cire haraji kan kayayyaki 7,315 daga Nijeriya, ƙarƙashin Yarjejeniyar Haɗin Gwiwar Tattalin Arziki ta Nijeriya da UAE (CEPA).
An rattaba hannu kan yarjejeniyar ne a ranar 13 ga Janairu, 2026, bayan tattaunawa mai zurfi da Ministar Kasuwanci ta Nijeriya, Dakta Jumoke Oduwole, ta jagoranta, tare da goyon bayan Ma’aikatar Shari’a da Hukumar Kwastom ta Nijeriya.
Ministan Harkokin Kasuwanci na UAE, Dakta Thani bin Ahmed Al Zeyoudi, ya sanya hannu a madadin ƙasarsa, a gaban Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Shugaban UAE, Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan.
Ma’aikatar ta bayyana cewa yarjejeniyar za ta buɗe sabbin kasuwanni ga kayayyakin Nijeriya, da kuma sauƙaƙa zuba jari daga ɓangarorin biyu, tana mai cewa wannan mataki babban jigo ne wajen zurfafa alaƙa ta tattalin arziki.
A ƙarƙashin yarjejeniyar, Nijeriya za ta cire haraji nan take kan kayayyaki 3,949 daga UAE, yayin da za a cire haraji a hankali kan wasu kayayyaki 2,294 cikin tsawon shekaru biyar. An cire wasu kayayyaki 123 daga tsarin sassauta harajin gaba ɗaya.
A nata ɓangaren, UAE ta soke haraji nan take kan kayayyaki 2,805 daga Nijeriya, yayin da za a cire haraji a hankali kan wasu kayayyaki 1,468 cikin shekaru uku, sannan wasu 3,042 cikin shekaru biyar. UAE ta ware kayayyaki 593 da ba za a sassauta musu haraji ba.
Gwamnatin Tarayya ta ce wannan sauyi zai buɗe kasuwar UAE ga kayayyakin noma da na masana’antu daga Nijeriya, ciki har da kifi da sauran kayan ruwa, hatsi, dabbobi da naman su, ‘ya’yan itatuwa, auduga, fata da sauran kayayyakin dabbobi. Haka kuma, za a cire haraji kan coco, kofi, shayi, man fetur da kayayyakin itace cikin tsawon shekaru uku zuwa biyar.
Ga ɓangaren masana’antu, UAE za ta soke haraji nan take kan magunguna, sinadarai, takarda, littattafai da jaridu. Kayayyakin injuna, motoci, kayan lantarki, tufafi, kayan ɗaki da kayan gini kuma za a sassauta harajinsu a hankali.
Sai dai UAE za ta ci gaba da hana shigo da wasu kayayyaki guda 35, ciki har da naman alade, miyagun ƙwayoyi, tayoyi da aka yi amfani da su da kuma kayayyakin da ke ɗauke da asbestos.
A ɓangaren Nijeriya kuma, za ta soke haraji nan take kan man fetur, injuna, motoci, kayan lantarki, ƙarafa da robobi daga UAE. Harajin kifi, ‘ya’yan itatuwa, kayan lambu da tufafi kuma za a sassauta shi cikin shekaru biyar. Nijeriya ta ware kayayyaki 123 masu muhimmanci da ba za a cire musu haraji ba, ciki har da nama, madara, wasu kayan lambu, man girki, coco da kayan sarrafa hatsi.
Gwamnati ta jaddada cewa jerin kayayyakin da aka haramta shigowa da su a Nijeriya na nan daram, kuma wannan yarjejeniya ba ta shafe su ba.
Baya ga kayayyaki, yarjejeniyar ta shafi ɓangaren ayyuka da zuba jari. Nijeriya ta amince da buɗe ɓangarori 99 na ayyuka, yayin da UAE ta amince da ɓangarori 108. Hakan zai bai wa ‘yan kasuwar Nijeriya damar shiga UAE domin neman damar kasuwanci da kafa kamfanoni ƙarƙashin kariyar doka.
Gwamnatin Tarayya ta ce yarjejeniyar za ta ƙarfafa shigowar jarin waje daga UAE zuwa Nijeriya, tare da kara matsayinta a matsayin cibiyar zuba jari a yankin ECOWAS da AfCFTA. Ta kuma tabbatar da cewa yarjejeniyar ta dace da ƙa’idojin WTO da sauran yarjejeniyoyin yankin da Nijeriya ke ciki.
A ƙarshe, gwamnati ta bayyana ƙwarin gwiwar cewa wannan yarjejeniya za ta samar da ayyukan yi, ƙara fitar da kaya, da kuma zurfafa haɗin gwiwar tattalin arziki tsakanin ƙasashen biyu.
