Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Jihar Yobe na ɗaukar matakai masu ƙarfi na sake gina tattalin arziki bayan shekaru na rikicin Boko Haram, inda gwamnatin jihar ke aiwatar da shirin gina kasuwanni na zamani a sassa daban-daban domin bunƙasa harkokin kasuwanci da samar da ayyukan yi.
Wata tawagar ’yan jarida daga gida da ƙasashen waje na rangaɗi a halin yanzu domin duba waɗannan sabbin kasuwanni, tare da ganin da idonsu yadda ake aza tubalin farfaɗo da rayuwar al’umma da rikici ya daɗe yana gallaza wa.
Rangadin, wanda gwamnatin jihar ta shirya, ya nuna muhimmancin shirin da Gwamna Mai Mala Buni ke jagoranta na zuba hannun jari a muhimman ababen more rayuwa domin tayar da harkokin kasuwanci, samar da ayyukan yi da kuma dawo da martabar rayuwar jama’a da rikici ya tarwatsa.
Kwamishinan Harkokin Cikin Gida, Yaɗa Labarai da Al’adu na jihar, Abdullahi Bego, wanda ya jagoranci rangazin, ya bayyana cewa wannan shiri shi ne ginshiƙin dabarar farfaɗo da jihar.
Ya ce gwamnatin jihar na kai manyan ayyuka kai tsaye zuwa kowane ƙaramar hukuma, daga ƙauyuka masu nisa har zuwa birane, domin samar da damammaki na gaskiya ga jama’a a wuraren da bege ya kusan gushewa.
ɗaya daga cikin manyan wuraren da aka ziyarta shi ne sabon Kasuwar Yunusari ta zamani, wadda aka kammala kuma ake ɗaukarta a matsayin abin koyi ga sauran kasuwannin da ake shirin ginawa a faɗin jihar.
Kasuwar ta ƙunshi shaguna guda 96, rumfunan sayar da kaya 146, shaguna da ɗakunan ajiya 46, da keɓaɓɓun shagunan nama, ginin gudanarwa, ofishin ’yan sanda, tashar kashe gobara da kuma ɗakin banki.
Kwamishinan Gidaje da Ci gaban Birane, Injiniya Ahmed Buba, ya bayyana cewa Yunusari ɗaya ce daga cikin cibiyoyin kasuwanci da ake shirin samarwa a tsarin sadarwa na tattalin arziki.
Ya ce an gina ko kuma an sabunta manyan kasuwanni a Damaturu, Potiskum, Gashua, Nguru, Ngalda, Buni Yadi, Yunusari da Geidam domin tabbatar da cewa babu wata al’umma da aka bari a baya.
Martanin jama’a game da wannan shiri ya kasance mai matuƙar armashi. Wasu mazauna yankin, Dama Usman da Sabo Saleh, sun bayyana cewa kasuwar ba gini kawai ba ce, illa wata alama ce ta sabuwar makoma.
Sun ce kasuwar za ta amfanar da al’umma, ta ja hankalin masu zuba jari, tare da zama tushen ci gaba mai ɗorewa ga yankin.
A cewarsu, wannan shiri ya nuna aniyar gwamnatin Buni na mayar da Yobe kan turbar ci gaba, tare da dawo da martabar tattalin arziki da zaman lafiya a yankunan da rikici ya daɗe yana addaba.
