Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Jihar Kano ta ce ta kammala horaswa tare da tallafa wa matasa 2,260 a fannoni daban-daban na sana’o’i, a wani yunƙuri na bunƙasa samar da ayyukan yi da ƙarfafa dogaro da kai a faɗin jihar.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana haka yayin bikin kammala horaswa da rabon tallafi ga waɗanda suka amfana da shirin, wanda aka gudanar a Gidan Gwamnatin Kano.
Gwamnan ya bayyana bikin a matsayin sabon babi ga matasan da suka ci gajiyar shirin, yana mai buƙatar su zama masu amfani ga tattalin arzikin jihar ta hanyar amfani da kwarewar da suka samu.
Gwamna Yusuf ya ce rabon tallafin ya nuna aniyar gwamnatinsa na bunƙasa rayuwar matasa, yana mai jaddada cewa an farfaɗo da cibiyoyin koyon sana’o’i da harkokin kasuwanci guda 26 da a baya suka lalace, domin inganta rayuwar matasa maza da mata a faɗin jihar.
Bayanan da aka fitar sun nuna cewa Cibiyar Horticulture, wadda ta taka rawa wajen horaswar, ta fitar da matasa 750 da aka horas a fannoni kamar shirye-shiryen kwamfuta, gyaran waya, saka na’urorin CCTV, fasahar hasken rana da sarrafa bayanai ta zamani. Haka kuma cibiyar ta horas da wasu matasa 750 kan bunƙasa gonaki da tsara shimfiɗar wuraren shaƙatawa, domin tallafa wa sabunta birane da kasuwanci.
Haka zalika, Cibiyar Tuki ta horas da matasa 750 a fannin tuƙi, kiyaye dokokin hanya da tsaron ababen hawa, da nufin ƙara damar samun aiki tare da inganta tsaron hanya a faɗin ƙasa.
Cibiyar Kiwo kuwa ta fitar da mutane 205 a zangonta na uku, wanda ya kai jimillar waɗanda aka horas zuwa 485, inda suka samu kwarewa kan hanyoyin kiwon dabbobi na zamani. Haka kuma Cibiyar Kifi ta fitar da wasu sabbin waɗanda suka kware a harkar kiwon kifi domin bunƙasa samar da abinci da tabbatar da tsaron abinci.
Gwamna Yusuf ya bayyana cewa kowane mahalarta shirin zai karɓi tallafin kuɗi na N50,000, yayin da waɗanda suka kammala horaswa a Cibiyar Tuƙi za su samu N100,000 sakamakon tsadar kayan aiki da ke tattare da sana’ar.
Ya ƙara da cewa, gwamnatinsa ta sanya gaba horar da matasa 50,000 a fannoni daban-daban na sana’o’i, domin ƙarfafa dogaro da kai da bunƙasa tattalin arzikin jihar cikin ɗorewa.
Gwamnan ya buƙaci matasan da suka amfana da shirin da su yi amfani da ƙwarewar da suka samu yadda ya kamata, domin gina makomarsu da kuma taimakawa ci gaban jihar Kano baki ɗaya.
