Saƙon 2026: Kungiyar Arewa ta buƙaci shugabanni su dawo kan tafarkin gaskiya

Spread the love

Daga DAUDA USMAN a Legas

Kungiyar Al’ummar Arewa ta ‘Arewa Community Forum’ da ke Legas ta aika da saƙo ga shugabanni da dattijan Arewa a farkon sabuwar shekarar 2026, inda ta buƙaci su kare muradun jama’a, su kuma cika alƙawuran da suka ɗauka a lokacin hawa mulki.

A cikin saƙon da Shugaban Kwamitin Amintattu na ƙungiyar, Alhaji Dr. Ibrahim Tanko, ya rattaba wa hannu, an bayyana cewa shugabannin yanzu sun taka rawa wajen raunana zaman lafiya, daƙile ci gaba, da kuma jefa Nijeriya cikin matsin lambar ƙasashen waje.

Ya yi nuni da matakin da Amurka ta ɗauka na ayyana Nujeriya a matsayin ƙasa mai matuƙar damuwa, yana mai cewa wannan abin kunya ne ga ƙasa da ta taɓa zama abin koyi a lokacin samun ‘yancin kai.

ƙungiyar ta kwatanta yadda shugabannin farko irin su Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato, suka yi aiki tuƙuru wajen bunƙasa ilimi da walwalar jama’a, musamman ta hanyar kafa makarantu da cibiyoyin horarwa da tsarin tallafin karatu.

An jaddada cewa Sardauna da takwarorinsa kamar Sir Kashim Ibrahim, Sir Abubakar Tafawa Balewa da Malam Aminu Kano sun yi shugabanci ne bisa kishin ƙasa da sadaukarwa, ba tare da son kai ko neman amfanin kansu ba.

Sakon ya nuna cewa a yau sassa da dama na tattalin arziki sun ruguje, lamarin da ya jefa miliyoyin yara cikin jahilci da rashin aikin yi.

An bayyana yadda wasu matasa suka faɗa tarkon tashin hankali sakamakon sakacin shugabanni, abin da ya haddasa asarar rayuka da lalacewar al’umma.

ƙungiyar ta ce wannan matsala ta samo asali ne daga karkatar da albarkatun ƙasa zuwa ayyukan siyasa da laifuffuka, yayin da makarantu da asibitoci ke durƙushewa.

An kuma zargi shugabanni da wawure kuɗaɗen mai, inda suka fifita jin daɗin kansu da zuba jari a ƙasashen waje maimakon raya ƙasa. 

Sakamakon haka, talauci ya ƙara ƙamari, yara suka koma tituna, yayin da ‘ya’yan masu mulki ke samun ilimi a ketare.

ƙungiyar ta ce, ana amfani da matasa marasa ilimi wajen biyan buƙatun siyasa, abin da ke ci gaba da jefa yankin cikin da’irar wahala.

ƙungiyar ta nuna damuwa kan yadda rashin tsaro ya hana yankin Arewa samun ci gaba, inda mutane ke mai da hankali ne kawai kan yadda za su tsira. Ta gargaɗi shugabanni cewa tarihi ba zai manta da irin wannan sakaci ba, tare da tunatar da su cewa akwai ranar hisabi a gaban Allah, inda mulki da dukiya ba za su amfanar da kowa ba.

Dr. Ibrahim Tanko ya ce saƙon ba na ƙiyayya ba ne, sai dai na neman lamiri, riƙon amana da adalci. Ya buƙaci shugabanni su koma kan tafarkin gaskiya, su fifita jama’a, su zuba jari a ilimi da tsaro, domin dawo da martabar Arewa da Nijeriya baki ɗaya.

Saƙon ya kammala da kira ga shugabanni da dattijai su zauki darasi daga shugabannin da suka gabata, su zama masu gaskiya da riƙon amana, domin ceto al’umma daga halin da ake ciki.

By ukarofi