Gidauniyar Manar El-Huda ta horas da mata kan kyautata zamantakewar aure

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

An bayyana mata a matsayin ginshiƙin tarbiyyar al’umma, inda kashi 80 cikin 100 na tarbiyyar yara ke fitowa daga hannunsu, yayin da iyaye maza ke bayar da kaso 20 cikin 100. Wannan ne ya sa ake buƙatar uwa ta gari domin a samu zuri’a mai cike da kyakkyawar tarbiyya.

Babban malamin addinin Musulunci, Farfesa Umar Sani Fagge, ne ya bayyana hakan a yayin jawabinsa a taron yaye mata da aka horas da su kan tarbiyyar zaman aure a ƙarƙashin Gidauniyar Manar El-Huda.

Taron ya gudana ne a makarantar firamare ta Fagge a ranar Asabar.

Farfesa Umar Sani Fagge ya shawarci iyaye mata da su mutunta kansu, su kula da mazajensu tare da bai wa ’ya’yansu tarbiyya ta gari, inda ya ce hakan ne zai haifar da natsuwa, zaman lafiya da albarka a rayuwar aure, tare da samun alheri a duniya da lahira.

Shugabar Gidauniyar Manar El-Huda, Malama Fatima Muhammad Fagge, ta bayyana wa manema labarai cewa taron ya ƙunshi manyan manufofi guda biyu. Na farko, cika addu’ar kammala saukar Alƙur’ani da ɗaliban makarantar Manar El-Huda suka gudanar domin roƙon Allah ya kawo zaman lafiya a ƙasa, ya albarkaci iyaye, mazajensu, ’ya’yansu, malamansu da al’ummar Annabi baki ɗaya. Ta ce an yi sauka har sau 12,000 kafin a gayyato Farfesa Umar Sani Fagge domin ƙare addu’ar.

Ta ƙara da cewa, taron ya haɗa da yaye mata 680 da aka bai wa horo na musamman kan zaman aure, ciki har da matan aure, zawarawa da ’yan mata, inda aka ba su shaidar kammala horon.

Malama Fatima ta ce sun fara wannan horo tun a shekarar 1439 Hijira da ya yi daidai da 2018 Miladiyya, kuma zuwa yanzu sun horas da mata fiye da 58,400. Ta bayyana cewa tasirin horon yana bayyana karara, inda maza kan kira su suna bayar da shaida kan kyakkyawan sauyi da suka gani a halayen matansu, har ma yara kan nemi su saboda canjin da suka gani a gidajensu.

Ta ce ba wai suna dogaro da ra’ayin ɗaliban su kaɗai ba, illa suna fi amincewa da shaidar mazaje, domin su ne ke ganin sauyi kai tsaye. Ta bayyana godiyarta ga Allah kan irin nasarorin da ake samu.

Ta ƙara da cewa horon yana ɗaukar tsawon watanni uku, wato makonni 12, sai dai idan wani abu ya samu cikas.

Game da karrama Farfesa Umar Sani Fagge, Malama Fatima ta ce sun yi hakan ne saboda matsayinsa na uba, malami, shugaba kuma mai tarbiyya da hangen nesa, inda ta ce duk kyautar da suka ba shi ta karramawa tana ganin ma sun rage masa girma.

Ta bayyana cewa Gidauniyar Manar El-Huda tana da makarantu 146 a faɗin jihar Kano, kuma suna shiga har ƙauyuka masu nisa domin kai wa mata wannan horo, duk da wahalar isa wuraren. Ta ce mazaje kan nuna godiya sosai saboda sauyin da suke gani a gidajensu, kuma sun kai wannan horo har jihohin Kaduna da Katsina.

Ta ara da cewa, suna da shirin zuwa gidajen mutane su horas da iyalansu kai tsaye idan aka gayyace su, domin gyara matsalolin zaman aure. Ta ce sun lura da cewa abubuwan da ke faruwa a yau a aure ba su dace da koyarwar Musulunci ba, don haka suke ƙoƙarin isar da sahihiyar koyarwar Annabi Muhammadu (SAW) a ko’ina.

Malama Fatima ta bayyana cewa suna ƙoƙarin tsaftace harkokin biki ta hanyar sauya waƙoƙin biki zuwa wa’azin zaman aure. Ta ce suna amfani da kalangu da waƙoƙi masu ma’ana domin isar da saon tarbiyya, wanda malamai ke tsara kalmomin da ake rerawa.

Ta ƙara da cewa, suna shirya kamun biki da tafi, addu’o’i, salati da karatun Alƙur’ani, tsarin da ya fara karɓuwa a Kano da wasu jihohi. Ta ce suna samun gayyata har daga Kaduna da Abuja, ciki har da gidajen gwamnati, domin shirya kamun amarya.

A ƙarshe, Malama Fatima Muhammad Fagge ta ce babu abin da ya fi ba ta daɗi kamar yadda Allah ke amfani da su wajen hidimar addinin Musulunci, kuma babban burinta shi ne Allah ya karɓi ayyukan da suke yi.

By ukarofi