Ana tursasa wa magoya bayanmu komawa APC a Kano – Kwankwaso

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce magoya bayansa a cikin gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf, na fuskantar matsin lamba kan shirin gwamnan na sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC.

A kan haka, jagoran na jam’iyyar NNPP, ya buƙace su da su rattaɓa hannun domin rage tashin hankalin da suka tsincin kan nasu a ciki.

Kwankwaso ya yi waɗannan makalaman ne a ranar Talata cikin wani sakon bidiyo da mai taimaka masa na kafafen sada zumunta, Saifullahi Hassan, ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Ana ganin yunƙurin Gwamna Abba na shiga APC ya jawo matsala a dangantakarsa da Kwankwaso, wanda ake wa kallon ubangidansa a siyasa.

Duk da cewa Kwankwaso ya ƙi kiran da ake yi masa na ya bi gwamnan zuwa APC, ya nuna damuwa kan rahotannin cewa ana tilasta wa zaɓaɓɓun shugabanni, ciki har da shugabannin ƙananan hukumomi, kansiloli, sakatarori, da sauran masu riƙe da muƙamai, su sa hannu a takardu da ke bayyana ɓangaren siyasar da suke goyon baya.

Ya ce: “Yau, 13 ga watan Janairu 2026, na iso jiharmu mai albarka ta Kano, inda na tarar da abubuwa masu kyau da dama, amma kuma akwai wasu abubuwa marasa daɗi, musamman batun tilasta shugabannin kananan hukumomi, kansiloli, sakatarori, da sauran masu muƙamai su rubuta ɓangaren da suke goyon baya, Kwankwasiyya ko Gandujiyya. Wannan abin takaici ne, kuma babu wani masoyinmu da zai ji daɗi da shi,” inji shi.

ƙoƙarin samun martanin gwamnati kan wannan zargi bai yi nasara ba jiya. Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Ibrahim Waiya, bai amsa kiran waya ba, haka kuma ba a sami mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature ba a lokacin da ake rubuta wannan rahoto.

Kwankwaso ya tuna yadda ƙungiyarsa ta Kwankwasiyya ta yi haƙuri har zuwa 2023 kafin ta dawo kan mulki a jihar.

Ya ce: “Mun yi haƙuri muka jira 2023, lokacin da jama’a suka fito suka jajirce suka zaɓi wannan gwamnati ta yanzu a jihar, da fatan samun rayuwa mai kyau, damar ilimi, ayyukan yi, da ayyukan raya kasa,” inji shi.

Kwankwaso ya bayyana siyasar Kano a matsayin fafatawa tsakanin “haske da duhu,” yana mai jaddada cewa tafiyar Kwankwasiyya tana da tsari bayyananne da ba za a iya lalata shi ba.

Ya ce: “Tafiyarmu, duk wanda ya shiga cikinta, sai ka bi tsarin ta. Amma idan ya kauce, sai dai ya sauya sheƙa. A Kano, muna da zaɓi biyu kawai: haske da duhu. Muna farin cikin cewa jama’a sun fahimci hakan sosai, kuma muna godiya gare su,” inji shi.

Game da shirin sauya sheƙar gwamnan, Kwankwaso ya ce rikicin ya jawo damuwa ga zaɓaɓɓun jami’an gwamnati a jihar.

Ya ce: “Tun da rikicin sauya sheƙa zuwa wajen Ganduje da Tinubu ya fara, mutane suka shiga damuwa da takaici. Shugabannin kananan hukumomi da dama sun kira ni ta waya; haka kuma wasu kansiloli da ke da damar yin magana da ni, sauran masu mukamai, da ’yan majalisar jihar da dama sun sanar da ni halin da suka tsinci kansu, inda wasu bas a iya barci, wasu ma har karin ruwa,” inji shi.

Kwankwaso ya ce ya yi shawara da manyan masu ruwa da tsaki, ya yanke hukuncin ba wa dukkan jami’an da ke cikin matsin lamba, ciki har da shugabannin kananan hukumomi, kansiloli zababbu da masu gafaka, da sauran zababbun jami’an gwamnati, damar bayyana goyon bayansu ga gwamnan na ɗan lokaci.

Ya bayyana wannan mataki a matsayin dabarar rage matsin lambar halin da suke ciki da kare jami’an da ke cikin barazana, tare da kiyaye sahihancin tafiyar gaba ɗaya.

Ya ce: “Mun san cewa ba a ma buga gangar siyasar 2027 ba. Magoya bayanmu su kasance a shirye. Mun san su duk inda suke, kuma su ma sun san mu. Ina ganin wannan zai taimaka wajen rage tashin hankali a jihar, musamman ga waɗanda ke cikin matsin lamba da barazana,” in ji shi.

Ya gode wa gwamnan bisa yabon da ya yi wa nasarorin gwamnatinsa a fili.

Ya ce: “Ina so in gode wa gwamnan jihar, wanda jiya ya yaba da gwamnatarmu kuma ya fallasa gwamnatin da ta lalata abubuwa da dama a jiharmu,” inji Kwankwaso.

A halin yanzu, APC a Jihar Kano ta ce ta kammala shirye-shiryen tarbar Gwamna Yusuf da sauran ’yan siyasa, tana mai cewa tana jiran fadar shugaban ƙasa ta saka rana.

Sakataren jam’iyyar na jihar, Ibrahim Zakari Sarina, ya bayyana haka jiya a cikin wata tattaunawa da manema labarai.

Ya ce a jam’iyyance, suna na’am da duk wani abu da zai ƙarfafa su kuma ya taimaka musu wajen samun nasara a zaɓe mai zuwa.

By ukarofi