NRG ta ziyarci JNI da CAN a ƙoƙarin ƙarfafa fahimtar juna a Arewa

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wasu manyan shugabanni daga Arewa, ciki har da tsohon kakakin NEF, Dr Hakeem Baba Ahmed, sun kai ziyara hedikwatar ƙungiyar Kiristocin Nijeriya ta jihohi 19 na Arewa da kuma Jama’atu Nasril Islam.

Ziyarar ta kasance ƙarƙashin wata sabuwar ƙungiya da aka kafa mai suna ƙungiyar Haɗin Kan Arewa ‘Northern Reconciliation Group’, wacce ta ƙunshi ‘yan Arewa Musulmi da Kiristoci da ke da manufa ɗaya ta ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kai.

Manufar ziyarar, a cewar jagororin tawagar, ita ce buɗe sabon babi na tattaunawa da fahimtar juna, domin kawo ƙarshen rikice-rikicen da suka daɗe suna addabar Arewa.

Dr Hakeem Baba Ahmed, wanda ya jagoranci tawagar, ya ce an kafa ƙungiyar Northern Reconciliation Group ne bisa fahimtar cewa Arewa ta sha wahala matuƙa sakamakon rikice-rikice da rashin jituwa.

Ya bayyana cewa ‘yan ƙungiyar sun haɗu ne a matsayin ‘yan Arewa, ba tare da la’akari da bambancin addini ba, domin su ɗaura yankin a turbar zaman lafiya da kwanciyar hankali.

A cewarsa, Musulmi da Kiristoci duk halittar Allah ne, kuma duk da bambancin aƙidu, an halicce su a matsayin al’umma ɗaya da ya kamata su zauna lafiya da juna.

Dr Hakeem ya jaddada cewa lokaci ya yi da Musulmi da Kiristoci a Arewa za su tsaya tsayin daka su zaɓi zaman lafiya maimakon rikici.

ƙungiyar ta fahimci cewa babu wata al’umma da za ta ci gaba idan tana fama da rabuwar kai, musamman ganin yadda rikice-rikice suka yi wa Arewa illa ta fuskar rayuka, dukiyoyi da ci gaban zamantakewa.

Ya ƙara da cewa, manufar wannan yunƙuri ita ce ƙarfafa fahimtar juna da gina amana tsakanin mabiyan addinai biyu.

Shugaban ƙungiyar Kiristocin Nijeriya ta jihohi 19 na Arewa, Joseph John Hayab, ya bayyana cewa ziyara irin wannan na da matuƙar muhimmanci ga makomar yankin.

Ya ce, duk da cewa an sha fuskantar faɗa da rashin fahimta a Arewa, yanzu akwai wata sabuwar murya da ke cewa ya isa haka, kuma dole ne a nemo mafita.

A nasa ɓangaren, Sakataren Janar na Jama’atu Nasril Islam, Farfesa Khalid Abubakar Aliyu, ya ce duk lokacin da mutane suka haɗa kai domin warware matsala, taimakon Allah kan zo.

Ya bayyana cewa JNI na maraba da wannan yunƙuri, yana mai jaddada cewa haɗin kai tsakanin Musulmi da Kiristoci ne ginshiƙin zaman lafiya mai ɗorewa.

By ukarofi