PDP ta tabbatar da rasuwar Mataimakin Gwamnan Bayelsa, Sanata Ewhrudjakpo

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Babbar jam’iyyar adawa (PDP) ta tabbatar da rasuwar Mataimakin Gwamnan Jihar Bayelsa, Lawrence Oboraw-Harievwo Ewhrudjakpo a jiya Alhamis.

An shiga damuwa da fari a ranar yayin da aka samu rahotannin da ke cewa ya yanki jiki ya faɗi a ofishinsa kuma an garzaya da shi asibiti.

Da take tabbatar da rasuwarsa a daren Alhamis wayewar Juma’a, PDP tsagin jagorancin su Turaki ta bakin Sakataren yaɗa labarai, Ini Emembong, ta bayyana rashin a matsayin abin da ya girgiza jama’a.

Sannan, ta bayyana marigayin a matsayin mamba mai biyayya, wanda rashinsa ya haifar da babba giɓi ga ƴaƴanta a jihar.

Ta kuma yi masa fatan samun yafiyar ubangiji tare da miƙa gaisuwar ta’aziyyarta ga gwamnati da al’ummar jihar bisa babban rashin.

Zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton, gwamnatin jihar ba ta fitar da wani saƙo na musamman akan al’amarin ba.

Ewhrudjakpo ya kasance mataimakin gwamnan Bayelsa a ƙarƙashin Gwamna Douye Diri na jihar tun daga 2020 har zuwa rasuwarsa.

By Babaji