Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Jam’iyyar PDP ta buƙaci sanata mai wakiltar Kogi ta tsakiya Natasha Akpoti-Uduaghan, ta yi watsi da ƙoƙarin da mahukunta s zauren majalisar dattawa ke yi na hana ta komawa majalisar bayan cikar wa’adin dakatarwar da aka yi mata.
A cikin jawabin da sakataren yaɗa labaran PDP, Debo Ologunagba, ya fitar a ranar Talata, ta buƙaci Natasha ta yi watsi da shawarar da majalisar ta ba ta, ta koma ta cigaba da wakiltar al’ummarta a yayin da majalisar ke shirin dawo daga hutun da ta tafi a ranar 23 ga watan Satumba.
“Muna shawartar sanata Akpoti-Uduaghan ta yi watsi da batun magatakardar majalisar tare da shiryawa domin ta koma majalisar. Jam’iyyar PDP a kira ga shugabancin majalisar da ya tabbata ya bai wa Natasha damar dawowa bakin aiki tare da gudanar da aikin wakilci a matsayin zaɓaɓɓiyar sanata,” in ji jawabin.
Wannan kalamai na PDP na zuwa ne bayan wata wasiƙa da muƙaddashin magatakardar majalisar, Yahaya Danzaria ya aike mata yana mai sanar da ita cewa ba za ta iya dawowa majalisar ba saboda maganar na gaban kotu, kuma za ta iya dawowa ne kaɗai idan majalisar ta sake nazari kan lamarin ko kuma kotu ta yi hukunci.
Sanatar tun da fari ta rubuta wa majalisar tana mai sanar da ita cewa tana da shirin dawowa majalisar bayan ƙarewar wa’adin dakatar da ita da aka yi na wata 6.
Sai dai har zuwa yanzu ba ta ce komai ba tun bayan saƙon da magatakardar majalisar ya aike mata.
Wannan ya haifar da kokwanto na ko za ta yi biyayya ko za ta yi watsi da saƙon majalisar dattawa.
Jam’iyyar PDP ta yi Alla-wadai matakin da majalisar ta ɗauka tana mai bayyana shi a matsayin take haƙƙin mata.
“Rahoton da magatakardar majalisar dattawa kan sanata Natasha ya kawo maganar zargin da ake na take haƙƙin mata da ƙoƙarin murƙushe muryar mata kamar yadda ake zargin shugaban majalisar Godswill Akpabio, da musguna wa sanata Natasha,” a cewar sanarwar.
Jam’iyyar ta buƙaci shugaban majalisar, Godswill Akpabio, ya magance wannan zargi kuma a maimakon amfani da majalisar wajen yi wa Natasha barazana.
“PDP na neman shuugaban majalisar dattawa da ta warware zarge-zargen da ake mata na nemanamfani da majalisar wajen cuzgunawa da barazana domin nesanta Natasha daga majalisar.”
Sannan ta soki dakatarwar wata shida da aka yi wa sanatar, tana mai bayyana cewa matakin ya yi tsanani, ba adalci kuma hakan ya saɓa wa dokokin majalisar.
Jam’iyyar adawar ta gargaɗi magatakardar majalisar kan janye wasiƙar domin riƙo da kyakkyawan tsarin dimokraɗiyya.
“Jam’iyyarmu na kira ga magatakardar majalisar da ya janye wannan wasiƙa da kuma bin ƙa’idojin zama ɗan ba ruwana da ƙin guje wa barin a yi amfani da shi a siyasance wajen tauye dimokraɗiyya da tanadin dokar majalisar.”
PDP ta yi kira ga ƙasashen duniya da ƙungiyoyin kare dimokraɗiyya da ƙungiyoyin kare haƙƙin al’umma da sauran masu haɗa kai da su yi Alla-wadai da barazanar da ake yi wa Natasha.
