Raɗɗa ya zama ɗan takarar gwamnan Jihar Katsina ƙarƙashin jam’iyyar APC

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Jam’iyar APC ta tabbatar wa gwamnan jihar Katsina da zama ɗan takarar jam’iyar a zaɓen 2027.

Shugaban kwamitin zaɓen yan takarar daga uwar jam’iyar APC Dr Muhammad Maccido ya bayyana haka a Katsina lokacin da ya ke gabatar da gwamnan a gaban dubban ya’yan jam’iyar.

Tunda farko kafin ƙaddamar da gwamnan sai da shugaban kwamitin ya miƙa shaidar takara ga yan takarar kujerar majalisar jiha,ta ƙasa da ta dattijai waɗanda suka sami nasarar hayewa zuwa takarar a ƙarƙashin jam’iyar APC.

A jawabin sa shugaban kwamitin sasanci kuma tsohon gwamnan jihar Rt Hon Aminu Bello Masari ya bayyana cewa su tun kafin zaman sasancin suka yanke hukunci cewa a matakin takarar kujerar gwamna Dikko Raɗɗa za a sake yi.

A cewar Masari su a jihar Katsina tsintsiya maɗaurin ki ɗaya ne wanda hakan ya sanya jihar Katsina ta zama abin koyi.

Ya yi godiya ga yan takarar gaba ɗaya da waɗanda suka samu da waɗanda ma basu samu ba da irin dattaku da suka nuna.

Masari ya jawo hankali na ya’yan jam’iyar cewa wannan zaɓe na fidda yan takara mataki na farko ne, dole yanzu kowa ya tashi tsaye wajan tallata yan takara daga yanzu har zuwa zaɓen 2027.

Banda Aminu Bello Masari da ya halarci taron akwai tsohon gwamna Ibrahim Shehu Shema.

Saura sun haɗa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin siyasa da na ayyukan yau da kullun Ibrahim Kabir Masari da Hadiza Bala Usman.

By ukarofi