Rahoton aukuwar zanga-zanga a fadata saboda kisan manoma ba gaskiya ba ne, cewar Sarkin Gwoza

Sarkin Gwoza a Jihar Borno, Alhaji Mohammed Shehu Timta, ya ƙaryata rahoton da aka yaɗa a soshiyal midiya kan cewa wasu fusatattun mazauna yankin sun yi zanga-zanga a fadarsa saboda kashe wasu manoma da ‘yan Boko Haram suka yi a yankin.

Basaraken ya ƙaryata rahoton ne a tattaunawar da ya yi da jaridar Vanguard a ranar Talata.

A cewarsa, “Jita-jitar da ake yaɗawa a soshiya midiya cewa fusatattu a Gwoza sun mamaye fadata kan kisan manoma da garkuwa da wasu a baya-bayan nan, hakan ba gaskiya ba ne.”

Sarkin ya tabbatar cewa lalle ne ‘yan bindiga sun kashe manoma biyar yayin da suke gona a tsakanin garin Gwoza da Limankara da tsaunukan Tangerang a ƙarshen makon da ya gabata.

Ya ƙara da cewa, ‘yan bindigar sun yi garkuwa da wasu mutum uku, inda daga bisani suka kashe ɗaya daga ciki, sannan kawo yanzu babu labarin ragowar biyun.

Daga nan, ya nuna takaicinsa da aukuwar lamarin, wanda a cewarsa hakan ya sa al’ummar yankin ziyartar fadarsa domin jajantawa da kuma ta’aziyya.

Ya ce gaskiyar al’amari shi ne, Asabar da ta gabata ya tafi Maiduguri don halartar taron ƙaddamar da wasu ayyuka da gwamnan jihar ya yi albarkacin cika kwana 100 a ofis a wa’adin mulkinsa na biyu.

A nan “Na samu kira cewa ‘yan Boko Haram sun kashe mutanena biyar a gona, bayan kuma sun yi garkuwa da wasu mutum uku….”

“Na yi mamaki bayan ganawa cikin lumana da jama’ar da suka zo mini ta’aziyya, wasu mahassada suka shiga soshiyal midiya tare da yaɗa wai wasu fusatattun jama’a sun yi zanga-zanga a fadata.”