Daga AISHA ASAS
Wani lokaci a fina-finai, ba wai fuskar jarumi ko kalaman da ya faɗa ne kawai ke sa masu kallo su riƙa tunawa da shi ba. Kiɗan da ke rakiyar shigarsa, sautin da ke ƙara ƙarfin wani yanayi da kuma waƙar da ta zama alamar fim na iya zama wani ɓangare na abin da ya sa jarumin ya zauna a zukatan mutane. Wannan ne ya sa rasuwar fitaccen mai tsara kiɗan fina-finan Tamil, Deva, ta zama babban rashi ga masana’antar, musamman ga waɗanda suka san irin gudunmawar da ya bayar wajen gina sautin fina-finan Rajinikanth.
Deva, wanda cikakken sunansa shi ne Devanesan Chokkalingam, ya rasu a Chennai a ranar Asabar, 17 ga Oktoba, 2026, yana da shekaru 75. Rahotannin jaridun Indiya sun ce rasuwarsa ta biyo bayan bugun zuciya. Ya shafe kusan shekaru arba’in yana tsara kiɗa, inda ya yi aiki a fina-finan Tamil, Telugu, Kannada da Malayalam, tare da tsara kiɗa ga fina-finai sama da 400.
Bayan rasuwarsa, Rajinikanth ya je gidan marigayin da ke yankin T Nagar a Chennai domin yi masa bankwana na ƙarshe da kuma ta’aziyya ga iyalansa. Rahoton The Indian Express ya bayyana cewa jarumin ya isa gidan cikin yanayin alhini, inda ya tsaya gaban gawar Deva domin girmama wanda ya bayar da gudunmawa ga wasu daga cikin fina-finan da suka fi shahara a aikinsa.
A cikin fina-finan da Deva ya yi wa Rajinikanth kiɗa akwai ‘Annamalai’, ‘Baashha’ da ‘Arunachalam’. Waɗannan fina-finai ba su samu karɓuwa ta hanyar labari da rawar jarumai kaɗai ba; kiɗan da ya tsara ya taimaka wajen ƙarfafa yanayin fina-finan, musamman sautin da ke rakiyar shigar Rajinikanth a wasu muhimman lokuta.
A lokacin da yake kan ganiyarsa a shekarar 1996, Deva ya tsara kiɗa ga fina-finai 36 a cikin shekara guda. Wannan adadi ya nuna irin saurin aikinsa da kuma yawan buƙatar da ake da ita ga baiwarsa a wani lokaci da masana’antar fina-finan Kudancin Indiya ke ci gaba da faɗaɗa.
An kuma ba shi laƙabin Thenisai Thendral, ma’ana kamar iska mai sanyin kiɗa, wanda ya nuna irin yadda aka san shi a masana’antar. A tsawon aikinsa, ya haɗa waƙoƙin soyayya, kiɗan jarumta da kuma salon waƙoƙin da ke nuna rayuwar al’umma, har ya zama ɗaya daga cikin masu tsara kiɗa da suka bar tasiri a fina-finan Tamil.
Bayan rasuwarsa, wasu manyan mutane a masana’antar sun yi ta’aziyya, ciki har da Kamal Haasan da Vijay. Vijay ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga fina-finan Tamil, yana mai cewa waƙoƙin Deva za su ci gaba da kasancewa cikin tarihin masana’antar.
