“Jihar Katsina ta yi alƙawarin ɗaukar nauyin taron Ranar Marubuta wanda za a yi na gaba”
Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
A karo na uku, marubuta da manazarta adabin Hausa daga sassan nahiyar Afirka da Nijeriya sun yi haɗuwar yaushe rabo, a garin Dutse, Babban Birnin Jihar Jigawa, wanda aka gudanar a ranar 31 ga watan Disamba, 2025, domin ƙarfafa zumunci da tattauna hanyoyin inganta rubutun Hausa, don a duba yadda za a samar da haɗin gwiwa tsakanin marubuta da mahukunta, da nufin gano bakin zaren warware matsalolin tsaro da tattalin arziƙi da suke addabar wasu jihohin Arewa.
An zaɓi a yi taron ne a Jihar Jigawa, kamar yadda Sakataren Kwamitin Tsare-Tsare Dr Abdulrahman Aliyu ya bayyana, saboda ita ce kaɗai jihar da ba ta fuskantar wani ƙalubalen tsaro a shiyyar Arewa maso Yamma, kuma jihar da tattalin arziƙinta ke samun ƙarin haɓɓaka. Babu shakka wannan tunani da marubutan suka yi ya yi kyau, kuma da alamun ya yi matuƙar faranta ran hukumomin Gwamnatin Jihar Jigawa, waɗanda suka nuna amincewa da karɓar baƙuncin taron, tare da tabbatar da ganin taron ya samu nasara ba tare da fuskantar wata matsala ba.
Marubuta da manazarta harkokin adabi daga sassan Afirka, irin su Senegal, Nijar, da Kamaru, da kuma jihohin Nijeriya. Marubuta maza da mata daga Kano, da Jigawa mai masaukin baƙi, Kaduna, Katsina, Sakkwato, Zamfara, Kebbi, Neja, Filato, Bauchi, Gombe, Abuja, Taraba, da Adamawa sauransu, duk sun halarci wannan taro. Za a iya cewa, wannan shi ne babban taro mafi girma da marubuta da dama daga ɓangarorin adabi daban-daban suka halarta. An ƙiyasta taron ya samu halartar baƙi har kimanin mutum 200.
An fara gudanar da taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya ne a shekarar 2018 a Jihar Katsina, an yi na biyu a Jihar Kano a shekarar 2019, sai kuma na uku da aka yi na baya-bayan nan a Jihar Jigawa. Kodayake masu ruwa da tsaki a harkar adabi sun koka game da yadda aka samu jinkiri wajen cigaba da gudanar da taron duk shekara kamar yadda aka fara, wanda ya kai an samu ratar kusan shekaru huɗu a tsakani ba a sake haɗuwa ba. Abin da masana ke ganin bai dace ba, duba da irin tasirin da marubuta ke da shi ga cigaban al’umma.
Abubuwa muhimmai guda uku da taron ya fi mayar da hankali a kansu sun haɗa da gabatar da laccoci daga manyan baƙi, tattaunawar zaurukan baƙi na musamman akan wasu maudu’ai, sai miƙa shaidar samun nasara a Gasar Gajerun ƙagaggun Labarai da aka gudanar game da ƙagaggiyar fasahar zamani ta AI, wanda shi ne irinsa na farko. Sannan kuma an karrama wasu fitattun mutane da suka taimaka wajen samun nasarar taron, daga cikin manyan baƙi da ýan Kwamitin Tsare-Tsare.
A cewar jagororin taron, an zaɓi wannan jigo na AI ne a matsayin alƙiblar rubutun ƙagaggun labaran da aka sanya, domin zaburar da marubuta adabin Hausa wajen cigaba da bincike da neman hanyoyin cin moriyar fasahar AI, don inganta rubutun su.
Babban malamin adabi, Farfesa Mu’azu Sa’adu Muhammad Kudan daga Jami’ar Sule Lamiɗo dake Kafin Hausa a Jihar Jigawa, ya yi dogon bayani game da maudu’in sa na ‘Wane ne Bahaushe?’ Shaihun malamin ya kawo wasu bambance-bambance na ilimi game da hasashen da ake yi na asalin Bahaushe, da yadda harshen Hausa yake haɗiye wasu ƙananan harsuna da ya cuɗanya da su. Har ma ya yi wa harshen Hausa kirari da, Mesa Uwar Haɗiya!
Yayin da a ƙarshe ya rufe jawabinsa da jan hankali game da ƙalubalen da ake fuskanta na masu yaɗa ra’ayin ƙabilanci na Hausa zalla, wanda ya ce guba ce da ka iya gurɓata dangantakar dake tsakanin al’ummar Hausawa da Fulani waɗanda suka daɗe suna da rayuwa da auratayya tare da juna. Ya ce, wannan iƙirari nasu ba alheri ba ne ga Arewa, don haka hakki ne akan marubuta da ƴan jarida su yi rubuce-rubuce na wayar da kai, don ceto hankulan al’umma daga wannan gurɓataccen tunanin.
Harwayau, an saurari lacca ta musamman daga Farfesa Kanar Abubakar Surajo Imam, daga Kwalejin Horar Da Jami’an Soja ta NDA dake Kaduna, wanda ƙwararren Injiniya ne, kuma masanin harkokin tsaro. Ya gabatar da lacca cikin tsari da inganci game da ƙalubalen tsaro ga cigaban tattalin arziƙi, ta hanyar amfani da kafafen sadarwa na zamani da fasahar AI.
Ya shawarci marubuta da kada su ji tsoron zuwan fasahar AI wacce za ta iya rage tasirin basirar su ta ƙirƙira, amma za su iya amfani da ita wajen inganta rubutun da suke yi da bincike kan wasu muhimman abubuwa na ilimi. Sannan harwayau, ya ƙarfafa buƙatar watsa rubuce-rubuce game da asalin al’adar Hausawa da amfani da ingantacciyar Hausa, domin tsaftace tsarin fassara daga wani harshe zuwa wani, wanda akasari ake samun Hausar da ake gani daga AI ba ingantacciya ba ce. Ya nemi masu hannu da shuni su zuba jari a harkar inganta fasahar AI, yadda za ta amfanar da al’ummar mu da tsaron mu, don kare matasa daga samun ilimi ta gurɓatacciyar hanya.
A karon farko marubuta da dama sun yi ido biyu da sanannen malamin jami’ar nan masanin falsafa, Farfesa Bouba Namaiwa wanda asalin ɗan ƙasar Nijar ne, amma yana aikin koyarwa a Jami’ar Anta Diop dake birnin Dakar na ƙasar Senegal. Farfesan ya yaba wa marubuta na dauri waɗanda ƙoƙarin su da kishinsu a harshen Hausa ya ba da damar ƙirƙirar haruffan Hausa daga Larabci, wanda ya kai ga samun haruffan Ajami, kafin daga bisani a kai ga ƙirƙirar harruffan boko daga turancin Ingilishi.
Ya buƙaci marubuta su samar da rubuce-rubucen ilimi da suka shafi falsafa, kimiyya, da fasaha zuwa harshen Hausa domin taskace ilimi, da ƙara masa daraja. Yayin da ya gargaɗi al’ummar Hausawa game illar barace-barace, da ya ce tana zubar wa Bahaushe ƙima da daraja a idon duniya.
Taron ya kuma tattauna akan wasu zauruka na masana wanda suka yi tsokaci kan, ‘Rubutun Hausa a wajen ƙasar Hausa,’ wanda aka tattauna tsakanin wasu manyan baƙi daga Senegal, Nijar, da Kamaru, a game da tasirin harshen Hausa da al’adun Bahaushe a ƙasashen su. An kuma duba, ‘Rubutun Zube na Hausa a onlayin, ina aka dosa?’ Nan ma masana rubutun ƙagaggun labarai na Hausa irin su Hajiya Aisha Maimota, Hassana ɗanlarabawa, da Bamai Dabuwa, suka yi nazari kan muhimmancin rubutun Hausa da kuma ƙalubalen masu rubutun batsa a onlayin.
An tattauna kan, ‘Marubuta Mata A Jiya da Yau. Ina aka dosa?’ Ga kuma tattaunawar su Kabiru Yusuf Anka game da ‘Rubutun Gajerun Labaran Hausa: Ina aka fito? Ina ake? Kuma ina aka dosa?’ Yayin da aka yi tattaki cikin waƙoƙin Hausa, ɗaya daga cikin tattaunawar da ta ƙayatar da ni sosai.
Babu shakka an kwashi ilimi sosai a waɗannan zauruka da aka tattauna, wanda zai yi wahala ka samu irin ilimin da aka bajekolinsa a duk wani littafin Hausa da ake da shi a halin yanzu. Haƙiƙa masu tsara taron sun yi rawar gani wajen zaƙulo darussan da kuma manyan malaman da suka gabatar da tattaunawar akan, waɗanda akasarinsu malaman jami’a ne, ko marubuta da manazarta. Jinjina ga Dr Abdulrahman Aliyu, Malam Kabiru Yusuf Anka, Malam Ibrahim Indabawa, Shugaban Marubuta na Jihar Jigawa, Malam Hasheem Abdullahi, Dr Bilkisu Yusuf Ali, Hajiya Sadiya Garba Yakasai, Hajiya Umma Sulaiman (Aunty Baby) Malam Rabi’u Abu-Hidaya, da sauran duk waɗanda suka ba da gudunmawa wajen samun nasarar wannan taro.
Jinjina ta musamman ga wakilan Gwamnatin Jihar Jigawa ƙarƙashin Kwamishinan Watsa Labarai, Matasa da Al’adu, Honarable Sagir Ahmad Musa, da muƙarraban Gwamna Umar Namadi ɗanmoɗi da suka ƙarawa taron armashi, musamman hidimar da suka yi wa marubutan da suka samu nasara a gasar ‘Aiki Dai Malam’ da aka shirya kan ayyukan raya ƙasa na gwamnan jihar, da kuma na Gasar Ranar Marubuta Hausa ta Duniya na 2025.
Na shaida irin kai komo da wakilan Gwamnatin Jihar Katsina suka yi wajen tabbatar da ganin taron ya inganta, kuma marubuta sun samu tagomashin da ya dace. Jihar Katsina dai ta yi alƙawarin ɗaukar nauyin wannan taro na shekara-shekara wanda za a yi na gaba, za kuma ta cigaba da ɗaukar nauyin idan har ba a samu wata jihar da ta ɗauka ba.
