RTEAN ta horar da mambobinta kan dabarun shugabanci

Ƙungiyar masu motocin safa ta Nijeriya (RTEAN) ta sha alwashin inganta fannin sufuri ta hanyar daƙile duk wani nau’in dabanci da ake fuskanta a tashoshin mota a sassan ƙasa.

Shugaban RTEAN na ƙasa, Musa Maitakobi ne ya bayyana haka jim kaɗan bayan miƙa shahadar kammala samun horo na musamman game da shugabanci ga mambobin ƙungiyar su 17 a Jos, babban birnin Jihar Filato.

Yayin taron, shi ma shugaban RTEAN ɗin, an karrama shi da lambar yabo ta bajinta, wato “Nigeria Silent Heroes Award (NSHA)”.

Shugaban ya ce kundin tsarin mulkin RTEAN ba yarda da dabanci a harkokin ƙungiyar ba, don haka ya ce ilimin da mambobin da aka horar suka samu zai sauya tunanin da ‘yan ƙasa ke da shi kan ma’aikatan sufuri.

“Ina so in yi amfani da wannan dama wajen gode wa NIPSS. Wannan na da matuƙar amfani ga waɗanda suka samu horon.

“Da fari jama’a kan yi mana kallon ‘yan tasha, amma idan aka nazarci kundin tsarin mulkinmu, za a ga ba mu aminta da harkar daba a harkokinmu ba,” in ji shi.

Mataimakin shugaban RTEAN rehsen Jihar Kaduna kuma mataimakin shugaban RTEAN na ƙasa na shiyyar Arewa maso Yamma, Adamu Jalaludeen, na daga cikin waɗanda aka bai wa horon, ya ce ƙungiyarsu na neman zaunawa a gurbin da ya fi dacewa da ita a tsakanin takwarorinta.