Rumbun lantarki na ƙasa ya sake lalacewa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A karo na biyu Nijeriya ta sake fuskantar katsewar wutar lantarki sakamakon lalacewa da babban rumbun raba lantarki ya sake yi a yau Talata.

Wannan al’amari ya haifar da katsewar wutar lantarki a fannoni da dama na ƙasar ciki har da ofisoshi, guraben kasuwanci da masana’antun al’umma.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne rumbun wutar ya fara lalacewa, wanda shi karo na farkoa 2026 tun bayan samun ire-iren haka a 2025 a lokuta da dama.

Hukumomi sun alaƙanta lalacewa da tangarɗar na’ura da rashin cikakken gyare-gyare da kulawa ga manyan layukan wuta da ke raba wa sassan ƙasar.

Bincike ya nuna cewa dukkanin tashoshin samar da lantarki 23 da ke haɗe da babban layin sun daina aiki gaba ɗaya a sakamakon tangarɗar ta yau.

Kawo yanzu babu cikakken bayani akan musabbabin faruwar al’amarin kasancewar ba samu bayani na musamman daga hukumomin da abin ya shafa ba zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

By Babaji