Rundunar ’yan sandan Katsina ta bai wa iyalan jami’anta tallafin kuɗi

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina ta raba wa iyalai da magadan jami’anta da suka rasa rayukansu lokacin gudanar da ayyukansu cakin kuɗi na Naira Milyan 53 da dubu ɗari tara.

Da ya ke miƙa cakin kuɗin ga iyalai da  magadan ‘yan sandan su 25  a hedikwatar rundunar kwamishinan ‘yan sandan jihar Katsina Idris Dauda Dabban ya bayyana cewar bada cakin kuɗin wata Inshora ce da babban sufeto janar na ‘yan sanda Alƙali Baba ya ƙirƙiro da shi don tallafawa iyalan jami’an da su ka rasu lokacin gudanar da aiyukansu.

Ya ci gaba da cewa, an ɓullo da tsarin biyan magadan ne domin tallafawa rayuwarsu.

Daga nan sai ya yaba wa wannan yunƙuri na Sufeto Janar na ‘yan sandan ƙasar nan domin inganta rayuwar jami’an rundunar.

Ya kuma roƙi iyalan da su ka amfana da tallafin da su yi kyakkyawan amfani da kuɗin da aka ba su don bunƙasa rayuwarsu.

Da ya ke magana da majiyar Manhaja ta kamfanin dillancin labarai na Nijeriya a madadin waɗanda su ka amfana da tallafin Al’amin Nuradden ya gode wa babban Sufeton ‘yan sanda bisa ga tallafin ya kuma sha alwashin yin amfani da kuɗin da aka raba masu ta hanyar da ta dace.

By Editor