Ministan tsaron ƙasar Sin ya gabatar wa Amurka buƙatar Sin a fannoni 4

Spread the love

Daga CMG HAUSA

Yau ne, ministan tsaron ƙasar Sin Wei Fenghe, ya gabatar da jawabi kan ra’ayin ƙasarsa, game da odar yankin a yayin taron tattaunawa na Shangri-La karo na 19 da aka gudanar a ƙasar Singapore.

Dangane da hulɗar da ke tsakanin ƙasar Sin da ƙasar Amurka, ministan tsaron ƙasar Sin din ya ce, yanzu hulɗar da ke tsakanin ƙasashen 2 tana cikin wani muhimmin lokaci.

A ganin ƙasar Sin, kyakkyawar hulɗar da ke tsakaninta da Amurka ta dace da muradunsu da ma duniya baki ɗayan. A matsayinsu na muhimman ƙasashe 2 a duniya, ba za a iya raba haɗin gwiwar da ke tsakanin Sin da Amurka daga bunƙasar duniya cikin lumana ba. Yin fito-na-fito a tsakanin Sin da Amurka ba zai kawo musu da ma ƙasashen duniya alheri ba.

Ƙasar Sin tana adawa da ayyana ƙasashen 2 a matsayin masu takara da juna. Idan Amurka ta ci gaba da mayar da ƙasar Sin tamkar barazana, abokiyar takara, da ma abokiyar gaba, to, za ta yi mummunan kuskure.

Wei ya nuna cewa, ƙasar Sin ta buƙaci Amurka da ta dakatar da shafa mata kashin kaji, da neman daƙile ci gaban ta, kana ta daina tsoma baki a harkokin cikin gidanta, da kuma illanta muradun ƙasar Sin. A bayyane kasar Sin ta bayyana matsayinta, wato wajibi ne Sin da Amurka su tattauna da juna, su mutunta juna, su kuma yi zama tare cikin lumana, su haɗa kansu domin samun moriyar juna, amma idan Amurka tana son yin fito-na-fito da Sin, to, ƙasar Sin ba za ta ja da baya ba.

Fassarawa: Tasallah Yuan

By Editor