Za mu kashe Naira biliyan biyu kan tantance ma’aikatan makarantu – UBEC

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hukumar Kula da Makarantu a Matakin Farko (UBEC) ta ce, za ta kashe Naira biliyan biyu wajen tantance malaman makarantu a cikin kwana 10.

Babban Sakataren Hukumar UBEC, Hamid Bobboyi, ya ce, an ware kuɗaɗen ne domin tantance ma’aikatan makarantun a faɗin Nijeriya a shekarar 2022 da muke ciki.

Ya ce, hukumar za ta tantance makarantu a jihoi 17 na yankin Kudu da yankin Arewa mai jihohi 19 da kuma Birnin Tarayya, Abuja, daga ranar 4 zuwa 23 ga watan Yuli mai mkamawa.

Bobboyi ya shaida wa taron tantance ma’aikata da ya gudana a Abuja, inda ya ce, rashin cikakkun bayanana ma’aikatan makarantu babban ƙalubale ne ga wajen aiwatar da shirye-shiryen ilimi.

Don haka ya ce, tantance ma’aikatan ilimi da za a yi a bana zai ba da dama wajen samun cikakkun alƙaluma da sauran bayanansu.

Ya bayyana cewa, jami’an hukumar za su zaga makarantun firamare da ƙananan sakandare da ke matakin ilimi na bai-ɗaya domin gudanar a aikin a fadin Nijeirya.

A nasa jawabin, shugaban hukumar tantance ma’aikata ta ƙasa, Farfesa Bala Zakari, ya ce, hukumar ta tattaro adireshin ɗaukacin makarantun matakin farko a kowace ƙaramar hukumar da ke Nijeriya.

Ya ƙara da cewa, an yi hakan ne domin tabbatar da kai wa ga makarantun da ke wurare masu nisa da masu wuyan zuwa saboda matsalar tsaro da sauransu.