Masu sayar da GSM na Zamfara sun tabbatar da sace mutanensu 30 da ‘yan bindiga suka yi

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Ƙungiyar masu sayar da wayoyin hannu ta Jihar Zamfara ta tabbatar da cewa, wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mambobinsu kimanin 30.

Shugaban ƙungiyar, Comrade Kabir Garba Muktar ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Gusau a ranar Lahadi.

A cewarsa, an yi garkuwa da mambobinsu ne a tsakanin Turata zuwa Lambar Bakura a hanyarsu ta komawa Gusau yayin da suka halarci bikin auren abokinsu a Ƙaramar Hukumar Tambuwal ta jihar Sakkwato ranar Asabar.

“‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mambobinmu sama da 50 da misalin ƙarfe 6:00 na yammacin ranar Asabar a Ƙaramar Hukumar Turata da ke jihar Sakkwato amma 20 daga cikinsu sun tsere yayin harin,” inji shi.

Ya kuma yi kira ga Gwamnatin Jihar Zamfara da hukumomin tsaro a jihar da su ƙara ƙaimi domin ganin an ceto waɗanda lamarin ya rutsa da su lafiya.

Ya ce, “Muna kira ga Gwamnatin Jihar Zamfara da jami’an tsaro a jihar da su tabbatar an kuɓutar da mambobinmu lafiya daga hannun ‘yan ta’adda.”

Kazalika, Jami’in Huld’ɗa da jama’a na rundunar yansandan Jihar, SP Muhammad Shehu, a wata hira ta wayar tarho da Blueprint Manhaja ya tabbatar da faruwar lamarin.

A cewarsa, rundunar ba ta da cikakken adadin waɗanda aka yi garkuwa da su, amma sama da 20 daga cikinsu sun tsere sa’o’i kaɗan bayan ‘yan bindigar sun yi garkuwa da su a yayin harin.

SP. Shehu ya bayyana cewa, tuni aka tura tawagar bincike da ceto wurin domin tabbatar da ceto sauran waɗanda aka yi garkuwa da su lafiya.

Jaridar Blueprint Manhaja ta rahoto cewa ‘yan bindigar sun kai hari kan matafiya a kan babbar hanyar Sakkwato zuwa Gusau da ke Tureta zuwa Lambar Bakura, inda aka yi garkuwa da sama da mutane 50, musamman masu sayar da wayar hannu (GSM) na Bebeji Plaza a Gusau.