ACF ta yi Allah-wadai da kisan kiyashi a Owo

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ƙungiyar tuntuva ta Arewa (ACF) ta yi Allah-wadai da kisan da aka yi wa masu ibada a cocin St. Francis Catholic Church Owo da ke Jihar Ondo a ranar Lahadin da ta gabata, inda ta bayyana hakan a matsayin ɗaya daga cikin ɗabi’un dabbanci da mutane ke yi.

A yayin da ya ke kokawa kan yadda masallatai a Arewa suka sha fama da irin waɗannan hare-hare a baya, babban sakataren ƙungiyar ACF, Murtala Aliyu, ya ce, hare-haren na da nufin sanya ’yan Nijeriya gaba da juna, tare da yin kira ga ’yan ƙasar da su haɗa kai su tsaya tsayin daka wajen yaƙar wannan munanan ayyuka.

Ya kuma umarci jami’an tsaro da su tashi tsaye wajen tattara bayanan sirri da kuma sanya ido domin ba a amince da kashe-kashen da ’yan bindiga da ba a san ko su waye ba ke yi.

“Qungiyar tuntuva ta Arewa ta yi mamakin abin da ta ɗauka a matsayin mafi zalunci da rashin sanin yakamata, a ’yan kwanakin nan. Kisan bayin Allah da ba su ji ba ba su gani ba, a cocin St. Francis Catholic, da ke garin Owo na jihar Ondo, a makon farko na hidimar watan Yuni, za a iya kwatanta shi a matsayin zagon ƙasa marar misaltuwa da ya dabaibaye al’ummar ƙasar.

“ACF ta fusata a kan irin wannan harin na dabbanci da aka kai wa al’umma masu son zaman lafiya, inda aka yi asarar rayuka da dama, tare da jikkata dama inda yanzu su ke kwance a asibitoci. An yi irin wannan kashe-kashe a masallatai a jihohin Zamfara, Katsina, Sokoto, Kebbi da Kaduna, a yankin Arewa maso Yamma da jihohin Borno da Yobe a Arewa maso Gabas.

“Waɗannan hare-haren na cibiyoyi na ibada suna da nufin sanya wa masoyanmu masu son zaman lafiya gaba da juna.

“Ƙungiyar Arewa tuntuɓa ta Arewa za ta yaba da duk ƙoƙarin da aka yi wajen ganin an hukunta masu laifin. Ƙungiyar ba za ta ɗauki wani uzuri na danganta irin wannan mummunan aikin ga ‘yan bindiga kawai da ba a san su ba, yayin da muke zaune da muna cin abinci tare da masu aikata laifuka a cikin al’ummominmu. Ba abin yarda ba ne, a ƙyale irin wannan kashe-kashen da ba za a iya mantawa da su ba su faru ba tare da ƙulla wani rahoto na sirri wanda zai iya yaƙar hakan ba.

“Bari jami’an tsaronmu su maida hankali wajen ceto Nijeriya da rayuka masu kima. Asarar rayuwar ɗan Adam hasara ce ta ƙasa.

“Ƙungiyar tuntuva ta Arewa tana miƙa sakon ta’aziyya ga gwamnatin jihar Ondo, al’ummar Owo da kuma na kusa da iyalen waɗanda suka mutu, tare da addu’ar Allah ya basu lafiya,” inji magatakardar ACF.