Sabon layin dogo da ya zagaye hamada mafi girma a ƙasar Sin ya fara aiki

Daga CMG HAUSA

Alhamis din nan ne, aka fara aiki da sashin ƙarshe na layin dogo mai tsawon kilomita 2,712, wanda ya zagaye hamada mafi girma a ƙasar Sin, wato Taklamakan, dake yankin artewa maso yammacin jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta, bayan da aka shafe shekaru 3 da rabi ana ƙoƙarin ginawa.

Sabon sashin layin dogon mai nisan kilomita 825, ya tashi ne daga gabas da birnin Hotan zuwa gundumar Ruoqiang, kusa da gefen kudu da Taklamakan, hamada ta biyu mafi girma a duniya mai cike da yashi, inda kusan kashi 65 na layin dogo yake gudana cikin hamadar.

Buɗe layin dogo zai baiwa jiragen ƙasa damar zagaya da’irar hamadar dake zama karo na farko a duniya. Haka kuma, layin dogon zai sauƙaƙa jigilar kayayyaki da tsare-tsaren wasu sana’o’i dake yankin Xinjiang da suka haɗa da auduga, da dangin gyaɗa, da dabino, da ma’adinai.

A yau, fasinjoji sun yi tattaki zuwa tashar layin dogo da ke birnin Hotan, domin yin balaguro a karon farko a cikin wani jirgin ƙasa da ke gudun kilomita 120 a cikin sa’a guda, wanda kuma zai taimaka wajen sauƙaƙa tafiye-tafiye da inganta rayuwarsu.

Don taimakawa wajen kare hanyar dogon, an gina gadoji guda biyar, inda mafi tsayi daga cikinsu, ya kai fiye da kilomita 18, don daga layin dogon zuwa wani tsayin shinge wanda zai kare shi daga illar guguwar yashi.

Bugu da ƙari, an samar da wani ziri maras gurɓata muhalli, mai kusan murabba’in mita miliyan 50 na ciyayi, inda aka shuka bishiyoyi miliyan 13, waɗanda ake fatan za su ba da kariya ga sassan da ake ganin yashin zai iya yi musu illa.

Fassarawa: Ibrahim